Trump Ya Yi Baram Baram da Iran, Ya Kafa wa Tehran Sharadin Janye Takunkumi
- Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba zai sake tattaunawa da kasar Iran ba kuma ba zai ba ta wata dama ba
- Donald Trump ya ce sun riga sun lalata muhimman cibiyoyin nukiliyar kasar Iran a wani hari da suka kai
- Trump ya ce idan Iran ta nuna zaman lafiya da hadin kai, zai iya sassauta mata takunkumin tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ba zai sake tattaunawa da Iran ba kuma ba zai ba ta wata dama ko rangwame ba.
Shugaba Donald Trump ya bayyana haka ne sakamakon cewa sun dauki matakin lalata cibiyoyin nukiliyar kasar.

Asali: Getty Images
Trump ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a dandalinsa na Truth Social, inda ya caccaki tsohon shugaban Amurka, Barack Obama, bisa tattaunawar da ya yi da Iran a baya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Trump ya ce tattaunawa da Iran ta kare
Shugaba Trump ya yi bayani bayan Iran ta bayyana cewa ba za ta sake shiga tattaunawa da Amurka ba sai dai idan kasar ta tabbatar da cewa ba za ta sake kai mata hari ba.
A martanin Trump, ya ce:
“Ba zan bayar da wata dama ga Iran ba, sabanin abin da Obama ya yi. Ba zan yi magana da su ba tun bayan da muka lalata cibiyoyin nukiliyar su baki daya.”
Legit ta rahoto cewa Amurka da Isra’ila sun kai farmaki kan wasu cibiyoyin nukiliya na Iran, ciki har da Fordo, Natanz da Isfahan, lamarin da ya tayar da kura tsakanin kasashen.
Martanin kasar Iran ga Donald Trump
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Majid Takht-Ravanchi, ya bayyana cewa Amurka na bukatar bayyana matsayin ta game da hare-haren da take kaiwa, kafin a iya tattaunawa.
A wata hira da ya yi, Takht-Ravanchi ya ce:
“Ba mu amince da wani lokaci ko tsarin tattaunawa ba tukuna. Muna bukatar sanin ko Amurka za ta ci gaba da kai mana hari yayin da muke cikin tattaunawa.”
Ya kara da cewa Amurka ta nuna tana son komawa teburin sulhu, amma Iran ba za ta amince da hakan ba matukar za a iya kai mata hari ba tare da hujja ba.

Asali: Getty Images
Trump ya ce zai iya sassutawa Iran
Shugaban ya kara da cewa idan Iran ta daina barazana da nuna zaman lafiya, yana da shirin janye takunkumin tattalin arziki da aka kakaba mata.
Rahoton Middle East Monitor ya nuna cewa Trump ya ce:
“Idan Iran za ta daina barazana kuma ta kasance cikin lumana da hadin kai da Amurka, zan iya janye takunkumin da aka daura musu.”
Shugaba Trump zai shawo kan Iran da kudi
A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Donald Trump ya nuna sha'awar shawo kan kasar Iran ta hanyar kyautata mata.
An gano cewa Donald Trump zai yi kokarin samawa Iran Dala biliyan 30 domin dakile kokarinta na mallakar nukiliya.
Trump ya fara kokarin hakan ne kwanaki kadan bayan kawo karshen yakin Iran da Isra'ila da aka shafe kwana 12 ana yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng