Saudiyya Ta Fitar da Limamin da zai Yi wa Miliyoyin Musulmai Hudubar Arafa

Saudiyya Ta Fitar da Limamin da zai Yi wa Miliyoyin Musulmai Hudubar Arafa

  • Hukumomi a Saudiyya sun sanar da naɗin Sheikh Saleh bin Abdullah Al Humaid a matsayin limamin Arafa na shekarar 1446 bayan Hijira
  • Sheikh Saleh zai gabatar da hudubar Arafat daga Masallacin Namira a ranar 9 ga Zul-Hijjah 1446, yayin da alhazai ke gudanar da babban rukunin aikin Hajji
  • Saleh na ɗaya daga cikin manyan malamai a Saudiyya, mai cikakken tarihi da gogewa a fannin shari’a, koyarwa da shugabancin al'umma

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Saudi Arabia - Fadar masarautar Saudiyya ta sanar da cewa Sarki Salman, mai kula da Harami, ya naɗa Sheikh Saleh bin Abdullah Al Humaid a matsayin limamin Arafa.

Naɗin na zuwa ne yayin da alhazai daga sassan duniya ke shirin taruwa a filin Arafa domin sauraron huduba a ranar 9 ga Zul-Hijjah, wadda ke da matuƙar muhimmanci a aikin Hajji.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwar duba watan sallar layya a Najeriya

Arafa
Sheikh Al Humaid zai jagoranci hudubar Arafa a ranar 9 ga Dhul Hijja. Hoto: Inside Haramai
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da kasar Saudiyya ta wallafa a shafinta na X.

Tarihin rayuwa da karatun Limamin Arafa

Shafin masana fikihu na Saudiyya ya wallafa cewa an haifi Sheikh Saleh bin Abdullah Al Humaid a shekarar 1950 a garin Buraidah da ke lardin Qassim na Saudiyya.

Malamin ya haddace Alƙur’ani tun yana ƙarami, sannan ya yi makarantar firamare da sakandare a garin kafin ya koma Makkah domin cigaba da karatu.

Sheikh Al-Humaid ya kammala digirinsa na farko da na biyu a jami’ar Sarki Abdul Aziz a fannin shari’ar Musulunci, daga bisani ya samu digirin digirgir daga jami’ar Ummul Qura.

Sheikh Saleh bin Abdullah Humaid
Sheikh Saleh bin Abdullah Humaid yayin gudanar da huduba. Hoto: Inside the Haramain
Source: Facebook

Mukamai da limamin Arafan bana ya rike

Sheikh Saleh ya rike mukamai da dama a Saudiyya, ciki har da shugaban majalisar Shura a shekarar 1422 da shugaban babban kotun shari’a a 1430.

Ya wakilci Saudiyya a Hukumar Fiqhu ta Duniya tun daga 2007, inda daga bisani aka zabe shi a matsayin shugaban hukumar.

Kara karanta wannan

Sallar layya: kasar Saudiyya ta fitar da sanarwar duba jinjirin wata

Sheikh Saleh ya wallafa littattafai da dama, ciki har da na ilimin shari’a, hudubobi, da batutuwan zamantakewa da suka shafi aure da zaman lafiya.

Za a yi hudubar Arafa a Namira

A cewar sanarwar fadar mulkin, Sheikh Saleh zai gabatar da hudubar Arafa a masallacin Namira a ranar 9 ga Zul-Hijjah, 1446.

Alhazai daga ko’ina cikin duniya za su taru domin jin wannan muhimmiyar huduba, wadda galibi ke ƙunshe da saƙonni na ƙarfafa tauhidi, zaman lafiya, adalci da ɗa’a ga Allah.

Saudiyya ta bukaci a fara duba watan sallah

A wani rahoton, kun ji cewa kasar Saudiyya ta bukaci mutane su zauna cikin shiri domin fara duba watan Dhul Hijja.

Za a fara duba watan Dhul Hijja ne na bana domin shirye shiryen fara aikin Hajji da ranar salla da sauran lamuran da suka shafi addini.

An bukaci duk wanda yaga watan a kasar Saudiyya ya gaggauta sanar da kotu mafi kusa da shi domin tantancewa domin a sanar da jama'a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng