Saudiyya ta bayyana ranar Arfa da kuma Sallar Layya

Saudiyya ta bayyana ranar Arfa da kuma Sallar Layya

- Kasar Saudiyya ta bayyana ranar Litinin a matsayin ranar Arfa

- Washe garin ranar ita ce ranar Sallar Layya a fadin duniya

- Ba a ga jinjirin wata ba ranar Alhamis

Saudiyya ta bayyana ranar Arfa da kuma Sallar Layya
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Abubakar Sa'ad ke da hakkin bayar da sanarwar ganin jinjirin wata a Najeriya

Majalisar koli ta addinin Musulunci a Saudiyya ta sanar da ranar Litinin 9 ga watan Dhul-Hijjah 1437 a matsayin ranar hawan Arfa.

A wata sanarwa da majalisar ta fitar, a ka kuma lika a shafin Fatwa-online a Intanet, sanarwar bayyana cewa, majalisar ta yanke hukuncin ranar Lahadi 11 ga watan Satumba da zama 9 ga watan Dhul-Hijjah a matsayin ranar Arfa, yayin da ranar Litinin 12 ga watan Satumba da kasancewa ranar Sallar Layya.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, Majalisar ta yanke wannan hukunci ne a sakamakon rashin ganin jinjirin watan Dhul Hijja a ranar Alhamis a kasar, bisa ka’ida hukumomin Saudiyya ne ke da alhakkin sanar da ranar Arfa, wanda ke kawo karshen aikin Hajji na wannan shekarar, wanda hakan ke sa a yi Sallar Layya a sauran kasashen musulmai na duniya a washe gari.

Ana dakon sanarwar ganin watan ko akasin hakan daga Majalisar Koli ta kula da addinin Musulunci a Najeriya, wacce Mai alfarma Sarkin Musulmi ya ke jagoranta.

A baya dai an sha samun sabani a sanarwar ganin wata tsakanin hukumomin Saudiyya da na sauran kasashen musulmi, ciki har da Najeriya, wanda ya sa ayi bukuwan Sallar Layya, da dauka da kuma ajiye azumin watan Ramadana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel