Angola, Najeriya: Jerin Kasashen Afrika 7 da Suka Fi Yawan Matasa Marasa Aikin Yi

Angola, Najeriya: Jerin Kasashen Afrika 7 da Suka Fi Yawan Matasa Marasa Aikin Yi

  • Rashin aikin yi a tsakanin matasa ya karu a nahiyar Afrika sakamakon wasu dalilai na tattalin arziki, ilimi da sauransu
  • A shekarar 2024, mizanin rashin aikin yi a tsakanin matasan Afirka ya kai kaso 11%, inda har hakan ya haifar da zanga zanga
  • Legit Hausa ta gano cewa Afirka ta Kudu, Angola da Moroko, sun shiga cikin jerin ƙasashen Afrika da matsalar ta fi kamari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Saboda wasu dalilai na ilimi, zamantakewa da tattalin arziki, matasa a Afrika na fuskantar rashin aikin yi a mafi yawan kasashen nahiyar.

A shekarar 2024, an kiyasta cewa yawan matasan da ke zaman banza a Afrika ya kai kimanin kaso 11%. Matsalar ta fi tsanani a wasu ƙasashe.

Bincike ya nuna cewa matasa na fuskantar karuwar rashin ayyukan yi a kasashen Afrika
Afrika ta Kudu ce a sahun gaba a kasashen Afrika da matasansu ke zaman banza. Hoto: Jacob Wackerhausen, peeterv
Asali: Getty Images

Rahoton Saifaddin Galal da aka wallafa a shafin statista.com ya nuna cewa Afirka ta Kudu za ta samu mafi girman adadin matasa marasa yi a nahiyar a 2024.

Kara karanta wannan

Zargin karkatar da N111.8bn: Majalisar wakilai ta shirya bincikar gwamnatin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Binciken ya bayyana cewa kusan kaso 30 cikin ɗari na masu neman aiki a Afirka ta Kudu suna rayuwa ne ba tare da sun samu aikin ba.

Rashin aiki a tsakanin matasa ya tsananta

Duk da albarkatun ƙasa da kuma yawan matasa a Afirka, matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa ta kai wani mummunan matsayi a nahiyar.

Bisa ga rahoton Bankin Raya Afirka (AfDB), yawan matasan Afirka yana ƙaruwa da sauri kuma ana hasashen ya ninka zuwa sama da miliyan 830 nan da 2050.

“Daga cikin matasan Afirka kusan miliyan 420 masu shekaru 15-35, kashi ɗaya bisa uku ba su da aikin yi kuma sun karaya da nema.
Kashi ɗaya kuma suna cikin aikin da ba na dindindin ba, yayin da ɗaya cikin shida ne ke samun aikin da ake biyan su albashi mai dama dama.”

Kara karanta wannan

Rahoto: Manyan matsaloli 3 da suka hana yara miliyan 15 zuwa makaranta a Arewa

- Inji rahoton bankin AfDB.

Dalilin rashin ayyukan matasa a Afrika

Babban dalilin rashin aikin yi a tsakanin matasa a Afirka shi ne rashin haɗakar tsarin ilimi da bukatun kasuwar aiki.

Yawancin makarantun ilimi sun fi ba da fifiko ga ilimi a rubuce fiye da ilimi na kwarewar aiki a cewar rahoton Business Insider.

A wani rahoto da ya wallafa a mujallar The Conversation, Farfesa Stephen Onyeiwu ya yi iƙirarin cewa mafi yawancin matasan da ke tafiya ci rani ba su da ƙwarewar da ake bukata.

“Wannan rashin ƙwarewa ba matsala ce ta Najeriya kawai ba; ta yadu a duk Afirka. Wannan ya sa kusan kaso 80% na masu ci rani kan kare a Afirka maimakon zuwa Turai."

- A cewar Farfesa Stepehen.

Duk da cewa wasu ƙasashen Afirka na kokari wajen magance matsalar rashin aiki, amma matsalar na ci gaba da ƙara tsananta, wadda ke haifar da tashin hankali da zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gamu da sabuwar adawa mai zafi daga Arewa kan kudurin gyaran haraji

Kasashen Afrika 7 a rashin ayyukan yi

Rahoton shafin Trading Economics ya bayyana kididdigar matasa marasa aikin yi a ƙasashe bakwai na Afirka.

1. Afirka ta Kudu: 60.2%

Kididdigar rashin aikin yi a tsakanin matasa a Afirka ta Kudu, waɗanda suka haɗa da masu shekaru 15 zuwa 24, ya ragu zuwa 60.2% a zango na uku na 2024, daga 60.8% a baya.

Mizanin rashin aikin yi a tsakanin matasa a Afirka ta Kudu ya kai 56.23% daga 2013 zuwa 2024, ya kai kololuwar 66.50% a zango na uku na 2021 da mafi ƙanƙanta 48.80% a zango na huɗu na 2014.

2. Angola: 56.4%

Kididdigar rashin aikin yi a tsakanin matasa a Angola ya sauka zuwa 56.40% a zango na biyu na 2024, daga 63.50% a zango na farko na shekarar.

Matsakaicin adadin ya kasance 56.20% daga 2018 zuwa 2024, tare da kololuwar 63.50% a farkon 2024 da mafi ƙanƙanta 49.20% a zango na biyu na 2020.

Kara karanta wannan

'Arewa na fushi da kai': an gargadi Tinubu ya gyara tafiyarsa, yankin na neman mafita

3. Moroko: 39.5%

Kididdigar rashin aikin yi a tsakanin matasa a Moroko ya ƙaru zuwa 39.50% a zango uku na 2024, daga 36.10% a zango na biyu.

A matsakaici, adadin ya kai 22.01% daga 1999 zuwa 2024, inda ya kai kololuwa 39.50% a 2024 da mafi ƙanƙanta 13.10% a 2006.

4. Ethiopia: 27.2%

Adadin rashin aikin yi a tsakanin matasa a Habasha ya ƙaru zuwa 27.20% a 2022 daga 25.70% a 2020.

Matsakaicin adadin ya kai 24.33% daga 2009 zuwa 2022, tare da kololuwa 27.20% a 2022 da mafi ƙanƙanta 22.00% a 2016.

5. Cape Verde: 23.9%

Kididdigar rashin aikin yi na matasan kasar Cape Verde ya ragu zuwa 23.90% a 2023 daga 26% a 2022.

Matsakaicin adadin ya kasance 29.85% daga 2010 zuwa 2023, ya kai kololuwar 41.00% a 2016 da mafi ƙanƙanta 21.30% a 2010.

6. Rwanda: 18.8%

Kididdigar rashin aikin yi na matasa a Rwanda ya ragu zuwa 18.80% a zango na uku na 2024 daga 20.50% a zango na biyu na 2024.

Kara karanta wannan

Gombe: An rasa rayuka a rikicin makiyaya da manoma, an kona amfanin gona

Matsakaicin adadin ya kasance 22.33% daga 2019 zuwa 2024, inda ya kai kololuwa 29.80% a zangon ƙarshe na 2021 da mafi ƙanƙanta 16.60% a zangon farko na 2024.

7. Najeriya: 6.5%

Kididdigar rashin aikin yi na matasa a Najeriya ya sauka zuwa 6.50% a zango na biyu na 2024 daga 8.40% a farkon shekarar.

Matsakaicin adadadin ya kasance 21.40% daga 2014 zuwa 2024, inda kididdigar ta nuna matasa marasa aikin yi sun ragu sosai a wannan shekarar.

Neman aiki: Ganduje ya ba matasa shawara

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya bukaci matasan da ke shirin kammala digiri da su koyi sana'o'in dogaro da kai.

Tsohon gwamnan na Kano ya jaddada cewa ba kowa ne zai samu aikin gwamnati ba don ya gama karatu, don haka dole matasa su fantsama neman sana'ar hannu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.