Matar Aure Dake Zama Gida Daya da Mijinta da Saurayinta Tace Duniya Tayi mata Dadi

Matar Aure Dake Zama Gida Daya da Mijinta da Saurayinta Tace Duniya Tayi mata Dadi

  • Wata matar aure kyakyawa ta bayyana yadda take rayuwa a gida daya da saurayinta, mijinta da ‘ya’yanta biyu
  • Matar mai suna Tamica Wilder ‘yar asalin Byron Shire ce, kuma tun lokacin farko da suka hadu da mijinta tace ya barta ta shoshola
  • Bayan sun yi shekara 11 da aure, matar ta gabatarwa mijinta da saurayinta amma an dauka lokaci kafin su saba

Tamica Wilder mata ce da ta dawo da saurayinta gidan mijinta inda suke rayuwa tare da ‘ya’yanta.

Tamica Wilder
Matar Aure Dake Zama Gida Daya da Mijinta da Saurayinta Tace Duniya Tayi mata Dadi. Hoto daga Instagram / theorgasmicmama
Asali: Instagram

Alaka tayi karfi

A wani bayani da tayi, Tamica ta sanar da yadda ta hadu da mijinta shekaru 11 da suka gabata kuma ta sanar masa cewa tana da niyyar zama da shi amma ba shi kadai ba.

Kara karanta wannan

Jama'a sun shiga mamaki, dalibar jami'a a Najeriya ta haifi jarirai 5 nan take

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kamar yadda New York Post ta bayyana, ta na son zama ba da miji daya ba wanda tace ba zata sassauta ba amma ya ki ganewa da farko amma daga bisani ya fahimta.

Tamica ta yi bayanin yadda alakarsu ta cigaba da kamari saboda suna gwada abubuwa masu tarin yawa.

Bayan haihuwar yaranta maza biyu, ta samu saurayi a wani shagali da ta halarta.

A lokacin da ta je gida, ta sanar da mijinta labarin matashin da ta hadu da shi kuma tace bata da shirin barin shi.

“Bana son ya subuce min. Ina son kara ganinsa nan gaba. Akwai wani abu a tsakaninmu kuma abu ne da nake son bibiya.”

- Tace.

Ta cigaba da haduwa da saurayin har sai da ta shawo kansa ya dawo cikin iyalanta amma ta ce lamarin ba sauki gare shi ba. Ya kan kai yaranta su gan shi.

Kara karanta wannan

Auren Cin Amana Tsohuwar Matar Adam Zango Tayi, Jaruma Safna Ta Fasa kwai

Daga bisani sabon saurayinta ya samu fahimtar juna da mijinta sun kuma zama iyali daya yayin da suke shakawatarsu tare.

Yaran suna jin dadin yadda suke da iyaye maza biyu.

Auren Cin Amana Tsohuwar Matar Adam Zango Tayi, Jaruma Safna Ta Fasa kwai

A wani labari na daban, Sapna Aliyu Maru, jaruma a masana’antar Kannywood, ta bayyana yadda kawarta, Maryam AB Yola ta aure mata saurayinta duk da su na da kusanci.

A wata tattaunawa da tayi da Mujallar Fim, bayan daurin auren Maryam da kuma matashin mai suna Muhammad Murtala, ta ce an ci amarta ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel