Jerin Jihohin da ke da Mafi Yawa da Karancin Rashin Aikin Yi a Nigeria
- Hukumar NBS ta fitar da rahoto a kan mizanin rashin aikin yi a kasar
- Jihohin Imo, Adamawa da Cross Ribas ne ke da mafi yawan rashin aikin yi
- Osun, Benue da Zamfara ne jihohin da ke da karancin rashin aikin yi
Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) a ranar Litinin, 15 ga Maris, ta fitar da alkaluman bangaren Kwadago: Rahoton rashin aikin yi a zango na hudu na shekarar 2020.
Rahoton ya nuna cewa rashin aikin yi a Najeriya ya tashi zuwa kaso 33.3% a yayinda ake dubawa. Wannan yana nuna cewa a yanzu mutane miliyan 23 ba su da aikin yi a Najeriya.
KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa na kagi garkuwa da kaina, amaryar Kano
Wannan zaure ya lissafo jerin jihohi uku da abin ya fi shafa da kuma jihohi uku da abun bai shafa ba sosai.
Jihohin da suke da mafi yawan rashin aikin yi
1. Jihar Imo (56.64%)
2. Jihar Adamawa (54.89%)
3. Jihar Cross Ribas (53.65%)
Jihohin da ke da mafi karancin rashin aikin yi
1. Jihar Osun (11.65%)
2. Jihar Benue (11.98%)
3. Jihar Zamfara (12.99%)
Da take martani ga rahoton NBS, jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta zargi jam’iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) da yiwa ‘yan Najeriya karya game da dimbin ayyukan da gwamnatin tarayya ke samarwa.
PDP ta nuna cewa rahoton NBS kan karuwar rashin aikin yi a kasar nan ya tabbatar da cewa gwamnatin da APC ke jagoranta ba ta da gaskiya da ayyukanta a wannan batun.
KU KARANTA KUMA: Matsalarmu ba shugabancin 2023 bane, adalci muke so a yiwa mutane, Makinde
Wata sanarwa daga babban sakataren yada labarai na babbar jam’iyyar adawar, Kola Ologbondiyan, ya ce abin da ya fi muni ma shi ne yadda yawancin matasa ke rasa ayyukansu a karkashin wannan gwamnatin.
Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.
Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.
Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.
Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411
Asali: Legit.ng