Yadda Ficewar Nijar, Mali da Burkina Faso Daga ECOWAS Zai Kawo Matsaloli a Afrika
- Burkina Faso, Mali da Nijar sun fita daga kungiyar ECOWAS da aka yi shekaru kusan 50 ana tare
- Masana sun ce sauyin da aka samu a wannan kungiya mai tasiri yana da hadari ga yankin Afrikan
- Za a samu tawayar tattalin arziki saboda raguwar kasuwanci da kuma yiwuwar karin matsalar tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Ficewar Burkina Faso, Mali da Jamhuriyyar Nijar daga karkashin kungiyar ECOWAS yana da mummunan tasirin tattali.
Rahoton da aka samu daga Punch yace matakin zai nakasa kasuwancin kasashen yammacin Afrika da ya kai Dala biliyan 277.22.
Cinikin ECOWAS zai ragu a Afrika
Cinikin kayan da ake yi a duk shekara tsakanin kasashen da ke yankin yammacin nahiyar Afrikan ya zarce fam Dala biliyan 270 a yau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka alkaluman da aka samu daga shafin ECOTIS suka tabbatar a 2022, babu tabbacin ko cinikin ya karu daga lokacin zuwa yanzu.
Babban cibiyar kasuwanci na duniyar ta kan bibiyi cinikin da kasashe suke yi duk shekara. Atiku Abubakar ya yi tsokaci a kan batun.
ITC tana aiki ne da majalisar dinkin duniya da kungiyar WTO da Ngozi Okonjo-Iweala a yanzu, tana samun bayanai daga COMTRADE.
Masana sun yi fashin baki a kan halin ECOWAS
Masana sun shaidawa Daily Trust cewa rashin hulda da Mali, Burkina Faso da Nijar zai kawo tasgaro ta fuskar kasuwanci da tattali.
Yanke alaka da ECOWAS yana da mummunan tasiri da fuskar matsalar tsaro a Afrika musamman idan aka duba yanayin yankin Mali.
Farfesa Jibril Ibrahim ya bayyana cewa kungiyar ECOWAS da wadannan kasashe za su ga tasirin wannan matak nan da wani lokaci.
Masana sun ce ba a taba ganin alaka ta tabarbare haka ba tun 1975. Ana zargin matakin da Bola Tinubu ya dauka ba su taimaka ba.
Juyin mulki sun raba kan ECOWAS
Idan aka tafi a haka, kasuwancin da ake yi da kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar zai ragu a sakamakon juyin mulki da aka shirya.
Sojoji sun kifar da gwamnatocin da ke mulki a wadannan kasashe uku na Afrika.
Hambarar da gwamnatin farar hula ya jawo ECOWAS ta dakatar da kasashen daga 2021 zuwa 2023, yanzu sun zabi su fice gaba daya.
Asali: Legit.ng