Nyesom Wike: Ana Kukan Tsadar Rayuwa, Minista Yayi Karin Kudin Makarantu a Abuja

Nyesom Wike: Ana Kukan Tsadar Rayuwa, Minista Yayi Karin Kudin Makarantu a Abuja

  • Nyesom Wike ya amince a kara kudin da ake karba daga hannun makarantun ‘yan kasuwa
  • Matakin da Ministan ya dauko zai yi sanadiyyar tashin kudin karatu a makarantun Abuj
  • Wani jami’i a ma’aikatar ilmi yace karin da aka yi zai fara tasiri ne daga watan Junairun 2024

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A lokacin da ake kuka da tsada da kuncin rayuwa, Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya tsokano wani sabon fada.

Babu mamaki makarantun kasuwa suyi karin kudin karatu a sakamakon matakin da Nyesom Wike ya dauka inji jaridar Punch.

Nyesom Wike
Nyesom Wike ya kara kudin makarantu a Abuja Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

Abuja: Wike ya kara kudin makarantu

Babban ministan na harkokin Abuja ya yi kari kan abin da ake karba daga hannun makarantun ‘yan kasuwa da ke birnin tarayya.

Kara karanta wannan

Kalaman Buhari sun jawo za a binciki inda Gwamnoni 150 da Ministoci Suka Kai N40tr

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Takarda da ta fito daga ofishin shugaban sashen akanta a bangaren inganta nagartar aiki a ma’aikatar ilmi da ke Abuja ta nuna haka.

Mudi Muhammed yace karin kudin da aka yi zai fara tasiri ne daga watan Junairun 2024, Nairametrics ta kawo wannan rahoto yau.

Ministan Abuja ya kawo sabon tsari

Takardar tace a sakamakon na’am da sabon farashin da Mai girma Ministan Abuja ya yi, kudin ake karba daga makarantu ya canza.

Gwamnati tana karbar kudin shekara-shekara, tantancewa, kudin daukar dalibai da na sake tantacewa daga wadannan makarantu.

Matsayin masu makarantun kudi a Abuja

Sahara Reporters tace daga karshen Disamban bara, aka yi watsi da tsarin kudin da ake kai, amma makarantun sun yi tir da karin.

Kungiyar masu makarantun kasuwa sun ce bai dace ayi masu kari lokacin da gwamnati take neman rage haraji a kan al’umma ba.

Kara karanta wannan

An kama 1 daga kasurguman 'yan bindigan da suka sace Nabeeha da 'yan uwanta a Abuja

"Da wannan wasika ana sanar da ku cewa tsohon tsarin kudi ya daina aiki da 31/12/2023, sabon tsari zai soma aiki daga 1/1/2024."
"A karkashin sabon tsarin, ana karbar kudi ne gwargwadon kudin karantar da dalibi da kowane makaranta ta karba da adadin dalibanta."
"Saboda haka abin da kowace makaranta za ta biya ya sha bam-bam. Kuma a sani cewa kudin neman makaranta ya koma N40, 000 yanzu."

- Mudi Muhammed

An dauke ma'aikatan CBN daga Abuja

Ma’aikatan da ke bangarorin kula da bankuna, tsare-tsaren tattali da biyan kudi a CBN suna barin garin Abuja kamar yadda aka ji labari.

Sabon gwamna Yemi Cardoso ya dage kan batun rage jami’an da ke Abuja daga 4, 200 zuwa 3, 700. Yanzu wasu ma'aikatan sun koma Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel