Yanzu yanzu: An naɗa Okonjo-Iweala shugaban WTO

Yanzu yanzu: An naɗa Okonjo-Iweala shugaban WTO

- Mrs Ngozi Okonjo-Iweala ta zama mace ta farko kuma bakar fata da ta zama shugaban hukumar WTO

- Hakan na zuwa ne bayan wakilai daga kasashe 164 sun jefa kuri'a na amincewa da nadinta a matsayin shugaban hukumar

- Wa'adijn shugabancin Okonjo-Iweala zai fara ne daga ranar 1 ga watan Maris na 2021

An nada Mrs Ngozi Okonjo Iweala a matsayin shugaba Hukumar Cinikayya ta Duniya (WTO).

Sanarwar nadin Okonjo-Iweala ya fito ne daga bakin hukumar da ke Geneva a ranar Litinin 15 ga watan Fabrairu, The Cable ta ruwaito.

Okonjo Iweala ce mace ta farko kuma bakar fata da ta fara shugabancin hukumar.

Wa'adinta zai fara ne daga ranar 1 ga watan Maris na shekarar 2021.

DUBA WANNAN: Labari da ɗumi-ɗumi: Sanata Iyiola Omisore ya koma jam'iyyar APC

Yanzu yanzu: An naɗa Okonjo-Iweala shugaban WTO
Yanzu yanzu: An naɗa Okonjo-Iweala shugaban WTO. Hoto: @channelstv
Source: Twitter

Wakilai daga kasashe 164 da ke kungiyar ne suka jefa kuri'a kafin nadin na Okonjo-Iweala kamar yadda sanarwar da hukumar ta fitar.

DUBA WANNAN: Buhari bai taɓuka wani abin azo a gani ba a fannin tsaro, in ji Gwamna Ortom

An nada Okonjo-Iweala ne bayan sabon shugaban kasar Amurka Joe Biden ya goyi bayan nadinta wadda tsohon shugaba Donald Trump ya dakile.

Matakin na Biden wani mataki ne na goyon bayan hadin kai tsakanin kasashen duniya don warware matsalolin da ya shafi kasashen akasin tsarin Trump na 'Fifita Amurka' da ya janyo rikice-rikice na cinikayya.

A wani labarin daban, Rundunar Sojojin Nigeria ta nada Mohammed Yerima a matsayin sabon direktan sashin hulda da jama'a, The Cable ta ruwaito.

Yerima, mai mukamin Brigedier-Janar zai maye gurbin Sagir Musa wanda ya kasance kakakin sojin na rikon kwarya tun shekarar 2019.

Kafin nadinsa, Yerima ya rike mukamin direktan sadarwa na tsaro da kuma mataimakin direkta a hedkwatar tsaro.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Source: Legit.ng

Online view pixel