Magana ta Ƙare: Sojoji Sun Sanar da Hambarar da Bazoum a Juyin Mulkin Nijar

Magana ta Ƙare: Sojoji Sun Sanar da Hambarar da Bazoum a Juyin Mulkin Nijar

  • Mohammed Bazoum ya sauka daga kan karagar mulki bayan shekaru biyu a Jamhuriyyar Nijar
  • Sojojin kasar su ka bada sanarwar canjin gwamnati ta hanyar yin juyin mulki na bakwai a tarihi
  • Za ayi kokari wajen tsare lafiyar Shugaba Bazoum, yayin da sojojin su ka rufe iyakokin kasar

Niger – An cire Mohammed Bazoum daga kan karagar mulki a Nijar ta hanyar wani danyen juyin mulki da aka gudanar a ranar Larabar nan.

Rahoton da mu ka samu daga Reuters ya tabbatar da cewa wasu sojoji sun yi wa gwamnati tawage sun kifar da Shugaba Mohammed Bazoum.

A wata sanarwa da su ka fitar ta bakin Kanal Amadou Abdramane, sojojin sun sanar da cewa sun kawo karshen gwamnati mai-ci a kasar Nijar.

Nijar
Shugaban Nijar, Mohamed Bazoum Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Sojoji sun sanar da dalilin canjin iko

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Ali Nuhu Ya Taya Al'ummar Nijar Alhinin Halin Da Suke Ciki

A daren yau Amadou Abdramane ya karanto sanarwar tare da manyan sojoji tara a gefensa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi, Kakakin sojojin ya ce tabarbarewar rashin tsaro da rashin kyawun shugabanci da ake fama da shi ya jawo su ka yi juyin mulkin.

France 24 ta kuma tabbatar da sojojin sun rufe duka wasu iyakokin jamhuriyyar, sannan an kakaba dokar kulle tare da dakatar da duk ayyuka.

An gargadi kasashen Duniya

Sojojin sun ja-kunnen kasashen ketare, su ka nuna ba za su yarda wata kasar tayi masu katsalandan ba, tare da yin alkawarin tsare lafiyar Bazoum.

Zuwa yanzu ba a san halin da Mai girma Bazoum mai shekaru 63 yake ciki ba, sai dai da-dama daga mutanen kasar su na goyon bayan gwamnatin shi.

Manyan kasashen Duniya su na bukatar Jamhuriyyar Nijar domin su iya yakar ‘yan ta’addan da ke tada zaune tsaye a kasashen Mali da Burkina Faso.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: An Shiga Zullumi Yayin Da ‘Dogarai Suka Tsare’ Shugaban Kasa Bazoum Na Nijar, Karin Bayani

Amurka wanda ta kashe Dala miliyan 500 wajen tsamar da tsaro a Nijar daga 2012 zuwa yau , tayi kira ga sojojin da su yi gaggawar sakin shugaban.

Aljazeera ta ce Sakataren gwamnatin Amurka, Antony Blinken ya shaidawa manema labarai a New Zealand cewa ba su goyon bayan juyin mulki.

Tarihin juyin mulki a Nijar

Rahoton ya ce wannan shi ne juyin mulki na bakwai da aka yi a nahiyar Afrikar a cikin shekaru uku, wanda hakan yana da mummunan tasiri.

A tarihin kasar mai makwabtaka da Najeriya, Bazoum ne shugaban farko da ya gaji mulkin farar hula bayan shekaru fiye da 60 da samun’yancin kai.

An taba juyin mulki a Nijar a 1974, 1996, 1999 da kuma 2010, wannan ne karo na biyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel