Jerin Mutum 10 da Suka Fi Kowa Arziki da Adadin Dukiyarsu a Watan Junairun 2024

Jerin Mutum 10 da Suka Fi Kowa Arziki da Adadin Dukiyarsu a Watan Junairun 2024

  • Arzikin kasurguman masu kudi 10 da ake ji da su a duniya ya karu da $30 a farkon shekarar nan
  • Elon Musk yana da sama da $250b a lissafin Forbes, mai bi masa shi ne Bernard Arnault da danginsa
  • Bill Gates ya sauko a farkon 2024, Mark Zuckerberg mai kamfanin Facebook ya zarce shi da $3m

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Masu kudin duniya
Masu kudin duniya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Su wanene su ka fi kowa kudi a 2024?

1. Elon Musk

Elon Musk bai da sa’a a duniya a yau, mujallar Forbes ta ce shugaban kamfanin na Tesla da kuma dandalin X ya mallaki fam $251bn.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Attajirin Najeriya Dangote ya sullubo da aka fito da jerin farko na masu kudin 2024

2. Bernard Arnault

Bernard Arnault shi ne na biyu, ya yi arziki da harkar kwalliya. Shugaban na Louis Vuitton, Christian Dior da sauransu ya mallaki $197bn.

3. Jeff Bezos

Jeff Bezos wanda ya kafa Amazon tun 1994 yana cikin wadanda ake damawa da su har yau. Rahotanni sun ce yana da fiye da $172bn.

4. Larry Ellison

Dukiyar Larry Ellison ta ragu a sakamakon karyewar hannun jarin Oracle. Shi ne na hudu a duniya da $135.3bn, dukiyarsa ta ragu da $11bn.

5. Mark Zuckerberg

Mark Zuckerberg ya samu karin arziki sosai a halin yanzu, ya zama na biyar da bayan a watan Disamba shi ne na bakwai a duniya da $122m.

6. Bill Gates

A 1987 aka fara kawo Bill Gates a biliniyoyin da ake ji da su, daga 1995 zuwa 2017 ya sha gaban kowa, a Junairun nan ana lissafin yana da $119m.

Kara karanta wannan

Saura kiris da Buhari ya nada ni mukami a 2015, in ki karbar kujerar - Tsohon Minista

7. Warren Buffett

Tun yana yaro Warren Buffett ya san harkar kudi. Techeconomy ta ce tsohon mai shekara 93 ne na bakwai a duniya da sama da $120m.

8. Larry Page

Larry Page da Sergey Brin suka kafa Google a 1998 har yanzu yana cikin manyan kamfanin. Dukiyar Page ta zarce $116m a shekarar nan.

9. Sergey Brin

Kamar Larry Page, tsohon abokin aikinsa, Sergey Brin mai shekara 50 ya tara $111bn. yana cikin masu juya kamfanin Alphabet masu google.

10. Steve Ballmer

Steve Ballmer abokin karatun Bill Gates ne a jami’ar Harvard University kuma ya yi aiki a Microsoft. Attajirin da ya shiga NBA yana da $110m.

Attajiran duniya a 2023

A bara ana da labarin yadda Elon Musk ya sullobo ya ba Bernard Arnault wuri a jeringiyar mutanen da suka fi kudi na wani gajeren lokaci.

A lokacin ne aka ji cewa dukiyar Bernard Arnault nunka ta Bill Gates sau biyu har da doriya a sakamakon rabuwa da ya yi da mai dakinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel