Ana Tsoron Israila Ta Kai Hari a Iran, An Ji Fashe Fashe a Inda Aka Tanadi Nukiliya

Ana Tsoron Israila Ta Kai Hari a Iran, An Ji Fashe Fashe a Inda Aka Tanadi Nukiliya

  • An samu yamutsi a yankin Isfahan na kasar Iran a daidai lokacin da ake tunanin kasar Isra'ila zata iya kai hari ga kasar
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa yamutsin ya biyo bayan wani kara ne da aka ji a yankin da safiyar Jumu'a, 19 ga watan Afrilu
  • Hukumar da ke kula da makamashin nukiliya ta majalisar dinkin duniya ta tabbatar da ba a samu wata barna a yankin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kasar Iran ta harba wasu makaman bada kariya yayin da ta ji karar wani abu da ake zargin hari aka kawo a yankin Isfahan.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an ji karar ne a safiyar Jumu'a, 19 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Kungiyar tarayyar turai ta kakabawa Iran sabon takunkumi kan harin da ta kai Isra'ila

Iran Isra'ila
Gidan talbijin din kasar Iran ya ce ba a samu wata barna a yankin Isfahan ba.
Asali: Getty Images

Hakan na zuwa ne biyo bayan harin ramuwar gayya da Iran ta kai Isra'ila bayan harin da Isra'ila ta kai ofishin jakadancinta a Siriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Al-Jazeera ta ruwaito cewa an samu rahoton da ke nuna alamun Isra'ila ce ta yi yunkurin kai sabon hari a yankin na Iran.

Haka zalika rahotanni sun nakalto wani babban jami'in Amurka yana tabbatar da cewa Isra'ila ce ta kai harin amma har yanzu ba a samu tababcin hakan ba.

Yayin da Iran ke cigaba da tsananta tsaro a yankin Isfahan, an ruwaito cewa ta harbi jirage marasa matuka guda uku a yankin.

Ina ne Isfahan a kasar Iran?

Yankin Isfahan dai ya kasance tsakiyar Iran ne kuma nan ne cibiyar nukiliya watau makami mai linzami a kasar

A cewar kamfanin dillancin labarai na AP News, Isfahan wuri ne da Iran ke tanadin makamai ciki har da tashar makamin karkashin kasa.

Kara karanta wannan

Kasar Yarbawa: Kotu ta rufe masu fafutukar raba Najeriya bisa zargin cin amana

Isra'ila dai ta dade tana kokarin kai hari a Iran domin lalata Isfahan amma dai ba ta samu nasara ba.

Israila ta samu yin barna a Isfahan?

Hukumar kula da makamashin nukila ta majilisar ɗinkin duniya ta tabbatar da cewa babu wata barna da aka samu a tashar nukiliyar Iran da ke Isafahan.

Sai dai kawai karin matakan tsaro da Iran ta kara dauka a yankin ciki har da tsakaita zirga zirgar jiragen sama.

An lafta wa kasar Iran takunkumi

A wani rahoton kuma, kun ji cewa shugabannin kasashen turai (EU) sun kakabawa Iran takunkumi biyo bayan harin ramuwa da ta kai Isra'ila.

Kungiyar kasashen turai din ta ce dole ne su cigaba da ware Iran gefe har sai lokacin da ta fahimci kuskurenta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel