Takaitaccen tarihin rayuwa da arzikin Jeff Bezos, wanda ya ba $200b baya

Takaitaccen tarihin rayuwa da arzikin Jeff Bezos, wanda ya ba $200b baya

A zamanin yau, Duniya ba ta taba ganin mai kudi kamar Jeffrey Preston Bezos ba. Attajirin ya ba Dala biliyan 200 baya, ba a taba samun labarin mai irin wannan dukiya ba.

Legit.ng Hausa ta kawo maku takaitaccen tarihin Jeff Bezos bayan ya kafa wannan sabon tarihi:

1. Haihuwa

An haifi Jeff Bezos ne a garin Albuquerque, New Mexico a ranar 12 ga watan Junairu, 1964. Iyayensa Jacklyn (née Gise) da Ted Jorgensen marasa hali ne a lokacin haihuwarsa.

Mahaifinsa ya na da shago a kasuwa inda ya ke saida kekuna. Bezos ya na shekara hudu a Duniya, mahaifinsa ya rabu da mahaifiyarsa, daga nan ta auri wani mutumin kasar Cuba.

2. Karatu

Jeff Bezos ya yi karatun boko a garuruwan Houston da Miami. A 1986, Bezos ya samu shaidar digiri a harkar fasahar wutar lantarki a jami’ar Princeton University ta kasar Amurka.

3. Aiki

Bezos ya soma aiki ne a kamfanin Fitel, daga nan ya koma banki. A 1993, ya yi shawarar bude kamfanin Amazon, a dalilin haka ya bar wurin aikinsa ya fara wannan aiki a garejin gidansa.

Attajirin ya yi aiki da D. E. Shaw & Co inda ya zama daya daga cikin manyan kamfanin a shekara 30. An taba yi masa tayin aiki a kamfanoni irinsu Intel, Bell Labs, da Andersen Consulting.

4. Dukiya

A shekarar 1997, Bezos ya shiga cikin sahun Attajiran Duniya. Zuwa 1999, shugaban kamfanin na Amazon ya mallaki Dala biliyan 10. Tsakanin 2014 zuwa 2017, ya fara doke Bill Gates.

KU KARANTA: Messi ya ki zuwa filin wasan Camp Nou, ya na so ya bar Barcelona

Takaitaccen tarihin rayuwa da arzikin Jeff Bezos, wanda ya ba $200b baya
Arzikin Jeff Bezos ya na neman ya nunka na Bill Gates
Asali: Getty Images

A 2013, Bezos ya saye jaridar nan ta The Washington Post, bayan haka shi ne mai kamfanin jiragen Blue Origin.

5. Aure

A 1992 Bezos ya hadu da MacKenzie Tuttle lokacin ya na aiki da kamfanin D. E. Shaw. Bezos sun yi aure a 1993 har sun haifi ‘ya ya hudu. Daga baya Mc acKenzie ta rabu da attajirin.

6. Siyasa

Jeff Bezos ya na tsoma baki a sha’anin siyasar Amurka, a 2016 ya ki amincewa ya taimaka wajen yakin neman zaben Donald Trump. Tun daga nan su ke baram-baram da shugaban kasar.

Bezos ya bada gudumuwar makudan kudi wajen yakin neman zaben Sanatoci Patty Murray, Maria Cantwell da John Conyers, da kuma Patrick Leahy da Spencer Abraham.

7. Kyauta

Bezos ya taba bada kyautar $10, 000, 000, 000, $100, 000, 000, $300, 000, 000, $500,000, da $1, 000,000 a lokaci guda. Sai dai ana zargin cewa ya na kauracewa biyan haraji a Amurka.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel