Elon Musk Ya Sake Komawa Attajirin Da Ya Fi Kowa Kudi a Duniya, Dangote Ya Koma Matsayin Na 72
- Elon Musk ya sake komawa kan matsayinsa na attajirin da ya fi kowa kuɗi a duniya daga hannun Bernard Arnault
- Musk ya samu kusan $1bn inda ya doke Arnault daga matsayin na farko bayan Arnault ya yi asarar $5bn a ranar Laraba, 31 ga watan Mayun 2023
- Wanda ya fi kowa arziƙi a Najeriya, Aliko Dangote, ya koma matsayi na 72 a ranar Laraba bayan ya samu N24.4bn cikin kwana ɗaya
Shugaban kamfanin Tesla, Elon Musk, ya koma matsayin attajirin da yafi kowa kuɗi a duniya, inda ya karɓe kambun daga hannun ɗan kasuwar ƙasar Faransa Bernald Arnault.
Musk, wanda ya samu sama da $1bn cikin sa'o'i 24, ya karɓe kambun daga hannun ɗan ƙasar Faransan wanda ya riƙe kambun har na tsawon fiye da wata shida.

Asali: Getty Images
Kamfanin motocin Elon Musk ya samu tagomashi
Sabon shugaban na Twitter, ya samu wannan tagomashin ne bayan an siyar da hannun jarin kamfanin motocinsa na Tesla akan $203.93 a ranar Laraba, 31 ga watan Mayu 2023, wanda hakan ya sanya arziƙinsa ya kai $192 billion.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A na sa ɓangaren, Arnault ya koma matsayin na biyu ne bayan ya yi asarar $5bn cikin sa'o'i 24, inda arziƙinsa ya koma $187 bn.
Musk wanda yanzu haka yana ƙasar China domin tattaunawa da hukumomi kan matsayar motocinsa masu amfani da lantarki, ya tserewa Arnault da $5bn.
Dangote ya koma matsayi na 72 a jerin attajiran duniya
Haka kuma, attajitin da ya fi kowa kuɗi a Najeriya da nahiyar Afirika, Aliko Dangote, ya ƙara matsawa sama a cikin jerin attajirin duniya da mataki uku, a ranar Laraba, 31 ga watan Mayun 2023.
Hamshaƙin attajirin na Najeriya, yanzu yana a matsayi na 72 a cikin jerin hamshaƙan attajiran duniya, a cewar ƙididdigar Bloomberg.
Shugaban rukunonin kamfanin Dangote, ya samu $53.2m kusan N24.4bn a ranar Laraba inda ya koma matsayi na 75 da ya taɓa riƙewa a baya.
Legit.ng ta tattaro cewa Dangote ya koma na 75 ne bayan ya baro matsayi na 84 a cikin jerin attajiran na duniya a ranar Talata, 30 ga watan Mayun 2023.
Arzikin Dangote Ya Yi Tashin Gwauron Zabi
A wani rahoton na daban kuma, kun ji cewa arziƙin hamshaƙin attajirin da ya fi kowa kuɗi a nahiyar Afirika, Aliko Dangote, ya ƙaru sosai a cikin kwana ɗaya kacal.
Dangote ya samu $769m a cikin kwana ɗaya wanda hakan ya sanya ƙara matsawa sama a cikin jerin hamshaƙan attajiran da suka fi kowa kuɗi a duniya.
Asali: Legit.ng