Kungiyar Malaman Jami’a Ta ASUU Na Shirin Komawa Yajin Aiki

Kungiyar Malaman Jami’a Ta ASUU Na Shirin Komawa Yajin Aiki

  • Murna ta koma ciki yayin da kungiyar malaman jami'a ta bayyana yiwuwar komawa yajin aiki
  • Wannan na zuwa ne makwanni kadan bayan sulhu da gwamnati kan yajin da kungiyar ta shafe watanni takwas tana yi
  • Kungiyar malaman jami'an sun koka kan yadda gwamnati ta gaza biyan albashi da kari bayan sun kulla yarjejeniya

Najeriya - Yayin da daliban jami'a ke tsaka da doki da murnar komawa makaranta bayan watanni takwas suna zaune a gida saboda yajin ASUU, kungiyar ta ce za ta sake shiga yajin aiki.

Wannan na zuwa ne kasa da wata guda da kungiyar ta janye yajin aikin da ta fara tun watan Fabrairun bana, kamar rahotanni a baya suka bayyana.

Kungiyar ta koka kan yadda gwamnatin tarayya ta gaza cika alkawuran da ta dauka na gyara lamurran jin dadin malaman.

Kara karanta wannan

Sauya Naira: Muna Sanye da Ido Kan Gwamnoni 3 Dake Karagar Mulki, Shugaban EFCC

ASUU za ta koma yajin aiki
Kungiyar malaman jami'a ta ASUU na shirin komawa yajin aiki | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Mataimakin shugaban kungiyar ASUU, Dr Chris Piwuna, ya tattauna da BBC Hausa, inda ya bayyana musu halin da kungiyar ke ciki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya shaida cewa, ya zuwa yanzu dai kungiyar na shirin yanke shawarwari kan abubuwan da suka dace don kawo mafita ga bukatunsu.

Dalilin korafin malaman jami'a na ASUU

A cewarsa, malaman jami'an na ci gaba da bayyana korafinsu ne kan gazawar gwamnati wajen ba su albashin watanni takwas da suka yi a lokacin yajin aiki.

Hakazalika, ya bayyana balo-balo cewa, gwamnati bata cika ko daya daga alkawuran da ta dauka ba ga malaman, kamar yadda ya shaidawa BBC Hausa.

Hakazalika, ya ce babu wani kari na albashi da gwamnati ta tabbatar kamar yadda ta yi alkawari tun farko.

Lakcarori Zasu Sha Jar Miya, FG Ta Basu Albashin Rabin Wata

A wani labarin, gwamnatin tarayya ta biya lakcarorin jami’a dake karkashin kungiyar malamai masu koyarwa ta ASUU albashin kwanaki 18 na watan Oktoba, Legit.ng Hausa ta tabbatar da hakan.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Bude Wa Mutane Wuta Ana Tsaka da Cin Kasuwa, Sun Tafka Barna a Jihar Arewa

Lakcarori da dama da Legit.ng Hausa ta tuntuba sun tabbatar mata da hakan inda suka ce an biya su rabin albashinsu ne kuma yana nuna na watan Oktoba.

An rahoto yadda malaman jami’an suka koma yajin aikin watanni takwas da suka yi a ranar 14 ga watan Oktoban 2022. An yi kira ga lakcarorin da su koma bakin aiki a ranar da aka janye yajin aikin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel