An Bayyana Abinda Ya Haddasa Mutuwar Sarauniyar Ingila Queen Elizabeth II

An Bayyana Abinda Ya Haddasa Mutuwar Sarauniyar Ingila Queen Elizabeth II

  • A ranar 29 ga watan Satumba, 2022 aka bayyana takaradar shaidar mutuwar Sarauniya mafi daɗe wa a tarihin masarautar Ingila
  • Takardar ta bayyana cewa Sarauniya ta rasa rayuwarta ne sandiyyar tsufa, ta mutu tana da shekara 96 a duniya
  • Sarauniyar wacce ta shafe shekara 70 a karagar mulki ta mutu ne ranar 8 ga watan Satumaba, 2022 a fadar Balmoral

Musabbabin abinda ya haddasa mutuwar Basarakiyar Birtaniya, Sarauniya Elizabeth ta II ya bayyana. A bayanan da ke ƙunshe a takardar shaidar mutuwarta, ya nuna cewa tsufa ne ya yi ajalin Sarauniya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Sarauniya Elizabeth ta II ta mutu ne tana da shekaru 96 a duniya a fadar Balmoral yayin da iyalan gidan Sarautar ke kewaye da ita a farkon watan nan.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnan PDP ya sha dakyar, kotu ta kori takarar da ke neman rushe sahihancin takararsa

Queen Elizabeth II.
An Bayyana Abinda Ya Haddasa Mutuwar Sarauniyar Ingila Queen Elizabeth II Hoto: dailytrust
Asali: UGC

A takardar shaidar da National Records of Scotland ta fitar ranar Alhamis, 29 ga watan Satumba, 2022, marigayya Sarauniya ta mutu ne da ƙarfe 3:10 na yamma ranar 8 ga watan Satumba, 2022 a Fadar Balmoral, Ballater.

Musabbabin abinda ya haddasa mutuwar Sarauniya shi ne tsufa kamar yadda ka rubuta ɓaro-ɓaro a takardar kuma masarautar Ingila ta rattaɓa hannu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Labarin mutuwar Saraunuya ya fito ne a wata sanarwa da Masarautar Ingila ta fitar a madadin iyalan Elizabeth ta II.

"Sarauniya ta mutu cikin kwanciyar hankali a fadar Balmoral da yammacin nan. Sarki da Sarauniya za su zauna a Balmoral da yammaci kuma gobe za su koma Landan," inji Sanarwan.

Elizabeth II ta kwashe shekara 70 a gadon sarauta

Mutuwarta ya kawo karshen shekaru 70 da ta yi a karagar mulki, Basarakiya mafi daɗe wa a tarihin masarautar Ingila. Ta karɓi mulki ne bayan mutuwar mahaifinta Sarki George na IV a ranar 6 ga watan Fabrairu 1952.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Lawan Ya Bayyana Matsayinsa Kan Hukuncin Kotu Na Ba Wa Machina Takarar Yobe Ta Arewa

An haifi marigayya Elizabeth a ranar 21 ga watan Afrilu, 1926 lokacin mulkin Kakanta, Sarki George na V. Queen Elizabeth II ta zama Sarauniya mafi daɗe wa a karagar mulki.

An yi shagalin murnar cikar Sarauniya Elizabeth ta II shekara 70 a kan sarauta ranar 6 ga watan Fabrairu.

A wani labarin kuma Allah Ya Yiwa Sarkin Lokoja, Jihar Kogi, Dr Muhammadu Maikarfi, rasuwa

Dr. Muhammadu Kabir Maikarfi III ya rasu ne ranar Laraba a birnin tarayya Abuja bayan gajeruwar rashin lafiya da yayi.

Majiyoyi sun bayyana cewa za'a yi jana'izar mamacin ne ranar Alhamis, 29 ga watan Satumba, 2022 a Lokoja, babbar birnin jihar Kogi misalin karfe 4 na yamma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel