Lawan Ya Bayyana Matsayinsa Kan Hukuncin Kotu Na Ba Wa Machina Takarar Yobe Ta Arewa

Lawan Ya Bayyana Matsayinsa Kan Hukuncin Kotu Na Ba Wa Machina Takarar Yobe Ta Arewa

  • Dr Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawan Najeriya ya ce ya amince da hukuncin kotu kan batun takarar sanata na Yobe ta Arewa
  • Lawan, cikin sanarwar da ya fitar ya ce ya tuntubi abokansa na siyasa da magoya baya kuma sun yanke shawarar ba zai daukaka kara ba
  • Lawan ya kuma mika godiya ga wasu jiga-jigan jam'iyyar APC a Yobe ya kuma yi wa mutanen mazabarsa alkawarin zai cigaba da musu hidima

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmada Lawan ya ce ya amince da hukuncin kotu na tabbatar da Bashir Machina a matsayin dan takarar sanata na Yobe ta Arewa a karkashin jam'iyyar APC a zaben shekarar 2023, The Cable ta rahoto.

A ranar Laraba, kotun tarayya ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta amince da Machina a matsayin halastaccen dan takarar APC na Yobe ta Arewa.

Kara karanta wannan

Atiku, Kwankwaso, Da Sauran Yan Takara Sun Hallara Wajen Yarjejeniyar Zaman Lafiya, An Nemi Tinubu An Rasa

Ahmad Lawan
Lawan Ya Bayyana Matsayinsa Kan Hukuncin Kotu Na Ba Wa Machina Takarar Yobe Ta Arewa. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

A baya, INEC ta fitar da jerin sunayen yan takarar zaben 2023 amma babu dan takarar sanatan APC na yankin.

Na yi shawara, ba zan daukaka kara ba - Ahmad Lawan

A cikin sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Lawan ya ce bayan tuntunbar abokansa na siyasa, ya yanke shawarar ba zai daukaka kara ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"A jiya, Laraba, 28 ga watan Satumban 2022, babban kotun tarayya a Damaturu ta yanke hukunci kan halastaccen dan takarar sanatan Yobe ta Arewa.
"Hukuncin ya ce ba ni ne halastace ba don haka shiga na zabe bai halasta ba.
"Bayan tuntubar abokai na na siyasa, magoya baya da masu fatan alheri, na yanke shawarar ba zan daukaka kara ba. Na amince da hukuncin."

Zan cigaba da bada gudumawa ga al'ummar mazaba ta da Jihar Yobe

Kara karanta wannan

Hotunan Motar Kudin Banki Da Ta Kama Da Wuta Tsakiyar Titi A Kebbi

Ya cigaba da cewa:

"A wannan matakin, ina son mika godiya ta ga mai girma, Sanata Ibrahim Gaidam bisa jagorancinsa a APC a Jihar Yobe. Ina kuma gode wa mai girma Gwamna Mai Mala Buni bisa goyon baya da yan uwantaka.
"Ga mazaba ta, ina muku godiya bisa goyon baya da tallafi a aikin mu na gina mutanen mu na mazabar Yobe ta Arewa da Jihar Yobe."

Daga karshe Lawan ya ce zai cigaba da bada gudunmawarsa da yi wa mutanensa hidima ko da baya rike da wani mukamin gwamnati kuma ya mika godiya ga Allah.

Kotu Ta Alanta Machina Matsayin Sahihin Dan Takarar Sanatan Yobe, Ta Yi Watsi Da Ahmad Lawan

A baya, kun ji cewa, Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Damaturu, jihar Yobe ta raba gardama tsakanin Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, da Hanarabul Bashir Machina.

Kotun ta umurci uwar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da Hukumar INEC su gaggauta sanya sunan Bashir Machina matsayin sahihin dan takaran kujerar Sanata mai wakiltar Yobe Ta Arewa a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel