Allah Ya Yiwa Sarkin Lokoja Rasuwa, Dr Muhammadu Maikarfi

Allah Ya Yiwa Sarkin Lokoja Rasuwa, Dr Muhammadu Maikarfi

  • Sarkin masarautar Lokoja ya rigamu gidan gaskiya bayan gajeruwar rashin lafiya da yayi
  • Za'a gudanar da jana'izarsa ranar Alhamis bayan Sallar La'asar a masarautarsa ta Lokoja
  • Marigayin ya rasu ne bayan kwashe shekaru talatin kan ragamar mulki

Abuja - Allah Ya yiwa Maigarin Lokoja dake jihar Kogi, Mai Martaba Alh. Dr. Muhammadu Kabir Maikarfi III, rasuwa.

Sarkin ya rasu ne yana mai shekaru 80.

Leadership ta ruwaito cewa Alh. Dr. Muhammadu Kabir Maikarfi III ya rasu ne ranar Laraba a birnin tarayya Abuja bayan gajeruwar rashin lafiya da yayi.

Maikarfi
Allah Ya Yiwa Sarkin Lokoja Rasuwa, Dr Muhammadu Maikarfi Hoto: Leadership
Asali: Facebook

Majiyoyi sun bayyana cewa za'a yi jana'izar mamacin ne ranar Alhamis, 29 ga watan Satumba, 2022 a Lokoja, babbar birnin jihar Kogi misalin karfe 4 na yamma.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Motar Fetur Ta Kama da Wuta, Mutane ‘Fiye da 20’ Sun Babbake Kurmus Nan-take

Maikarfi III ya hau mulkin Lokoja tun shekarar 1992.

Kwanakin baya yayi ikin murnar cikarsa shekaru 30 kan ragamar mulki.

Motar Fetur Ta Kama da Wuta, Mutane ‘Fiye da 20’ Sun Babbake Kurmus Nan-take

Duk a yau, fiye da mutum 20 ake tunani sun mutu a dalilin wata babbar mota da tayi hadari a kan wata gada a jihar Kogi.

Jaridar nan ta Daily Trust ta kasar nan ta fitar da wannan labari mara dadi a safiyar Alhamis, 29 ga watan Satumba 2022.

Rahoton yace babbar mota ta fadi ne a wa tagada da ke kan ruwan Maboro a karamar hukumar Ankpa a jihar Kogi.

Wannan mota ta dauka man fetur ne a lokacin da ta fi karfin direbanta, tayi hadari a kan titi.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Online view pixel