Ya Rabu Da Ni Saboda Na Shiga Aikin Soja, Jarumar Soja Tayi Magana da Tsohon Saurayinta

Ya Rabu Da Ni Saboda Na Shiga Aikin Soja, Jarumar Soja Tayi Magana da Tsohon Saurayinta

  • Wata kyakkayawar budurwa dake aikin Soja ta shiga duniyar TikTok da labarin abinda ya faru tsakaninta da saurayinta
  • Budurwar ya saki hotunan kanta cikin kayan Sojojin Najeriya da kuma lokacin da take farar hula
  • A cewarta, saurayinta ya yi watsi da ita saboda ta shiga aikin Soja, amma yanzu ta fi karfinsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wata Sojar Najeriya ta bayyana yadda wani saurayinta ya nuna mata kiyayya kawai don ta shiga aikin Soja.

Budurwar ta bayyana hakan ne yayinda ta saki hotunanta a manhajar TikTok sanye da kayan Soja.

A hoton farko, ta sanya hoton Soja tana tsugunne.

Sannan a wani hoto ta nuna yanzu tayi zurfi cikin harkar Soja, ta shiga 'Special Force'.

Soja Mace
Ya Rabu Da Ni Saboda Na Shiga Aikin Soja, Jarumar Soja Tayi Magana da Tsohon Saurayinta Hoto: TikTok/@horladayomi
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Rikicin addini ya barke tsakanin kirista da 'yan gargajiya, an kashe wani

Yan Najeriya sun bayyana ra'ayinsu kan wannan batu

Murjanatu Diri Tace:

"Nima aikin sojan nan hwa ina ganin yakamata na shiga kodan irin mazajen nan da basujin magana."

Uwanin Kinaya:

"Ai dole ya rabu dake Sbd kin san yawanci maxan arewa suna dukan matansu,,to kinga kekam idan yamiki ubanshi zakici."

Muhammad Buhari PA

"Lalle wanna ze Daku Idan Sukayi ido biyu da ita.
Dan Allah macen Soja kam mijin ta Yana nata Umurni kuwa"

Nasir Idris:

"Kibar shege, muna Nan a barracks"

Naseeba Adam Ibrahim:

"Se aikin Nan ya birgeni ko Dan muyi arangama da wani"

Ba Nasare:

tou ae kin Zama namiji Shi isa

Khalid Sani Khalid Sani

To ko nine zanzauna dake naje nabata miki rai kiyi rawar sukuwa akaina ,, kuma kada kuce INA tsoronta ..

Asali: Legit.ng

Online view pixel