Bidiyo: An kwantar da 'dan siyasa a asibiti bayan ya sha gurbattacen ruwa don birge jama'arsa

Bidiyo: An kwantar da 'dan siyasa a asibiti bayan ya sha gurbattacen ruwa don birge jama'arsa

  • Fitaccen 'dan siyasar Indiya na kwance magashiyyan a gadon asibiti bayan ya sha gurbataccen ruwa don birge magoya bayansa
  • A wani bidiyo da aka bayyana Bhagwanta Mann ya dauka kofin gilas tare da kwasar ruwa da kogi inda ya shanye a cikinsa ba tare da jinkiri ba
  • An gano cewa, kwatamin dattin birane da kuayukan kusa duk kogin suke gangarewa wanda ke cutar da jama'ar yankin

Babban ministan Punjab na Indiya, Bhagwant Mann, yana kwance magashiyyan a asibiti bayan ya sha gurbataccen ruwa daga wani kogi domin tabbatarwa da jama'a cewa ruwan tsaftatacce ne.

A wani bidiyo, an ga Mann ya debi ruwan a kofin gilas daga kogin kuma da kwankwade shi yayin da magoya bayansa suke masa ihu da yabo.

Babban ministan ya sha ruwan wanda a koyaushe yake gurbatuwa da kwatamin datti daga birane da kauyukan kusa ba tare da tabbatar da cewa tsaftatacce bane.

Kara karanta wannan

Bidiyon Ango Ya Zurfafa Cikin Tunani Yayin Da Amaryarsa Ke Girgijewa A Wajen Liyafar Aurensu

'Dan siyasa
Bidiyo: An kwantar da 'dan siyasa a asibiti bayan ya sha gurbattacen ruwa don birge jama'arsa. Hoto daga thenationeonlineng.net
Asali: UGC

Farfesan binciken zaman lafiya da tarzoma na Indiya, Ashok Swain, ya wallafa bidiyon 'dan siyasan yana kwasar ruwa daga kogin inda ya rubuta:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Babban ministan Punjab a bayyana ya sha gurbataccen ruwa daga kogi domin tabbatar da cewa tsaftacce ne. A yanzu yana kwance a asibiti."

Kalla bidiyon yadda lamarin ya faru:

Bidiyo: Ƴan achaɓa sun ritsa abokin aikinsu da yayi shekara 3 bai yi wanka ba, sun masa wanka a titi

A wani labari na daban, wani 'dan achaban kasa Ghana wanda ya yadu a kafafen sada zumunta kan tsabar kazantarsa ya ba mutane mamaki.

A bidiyon da ke ta yawo, an ga abokan aikinsa sun yi masa wankan dole a binar jama'a, @alreadyviralofficial suka wallafa bidiyon inda aka ga matashin yana kokarin kubcewa daga wurin wankan.

Wani mutum da ke rike da waya inda yake nadar yadda ake yi wa 'dan achaban wanka ya yi bayanin dalilin da yasa matasan suka dauka wannan matakin.

Kara karanta wannan

Bidiyon Shugaban APC na Kasa, Sanata Adamu, a Mimbarin Coci yana ihun 'Ku Yabi Ubangiji' ya janyo cece-kuce

Asali: Legit.ng

Online view pixel