Manyan masu kudin Afrika 5, yawan arzikinsu da yadda suka tara dukiyarsu

Manyan masu kudin Afrika 5, yawan arzikinsu da yadda suka tara dukiyarsu

  • Aliko Dangote, fitaccen mai arzikin da yafi kowa kudi a Afrika ya tsaya gyem a wannan jerin inda yake da kudi sama da $20 biliyan
  • Sauran sun fito daga kasashen Africa kuma sun mayar da hankali ne wurin zuba jari a fannin lafiya, abinci da wasanni
  • Jerin sunayen masu arzikin ya bayyana, yadda dukiyarsu ta kai wannan matakin tare da kayan kawa da suka mallaka har da agogunan hannu da sauransu

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Afrika tana kunshe da manyan masu kudi maza da mata wadanda suka tara tsabar dukiyarsu a fannoni daban-daban da suka hada da samar da ababen bukata, har da ma kayan abinci.

Kusan su biyar din sun bayyana a sabon jerin biloniyoyi 500 na duniya da Bloomberg ta fitar a 2021.

Manyan masu kudin Afrika 5, yawan arzikinsu da yadda suka tara dukiyarsu
Manyan masu kudin Afrika 5, yawan arzikinsu da yadda suka tara dukiyarsu. Hoto daga Bloomberg/ Contributor
Asali: Getty Images

Kamar yadda rahoton ya nuna, shugaban Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote, ya rike matsayi na farko a matsayinsa na wanda yafi kowa arziki a Afrika, karo na 11 a cikin shekaru 11 da yake matsayin kenan.

Kara karanta wannan

Tinubu da Shettima: CAN ta yi bore da martani mai zafi kan tikitin Muslmi da Musulmi

Yana da tarin arzikin da ya kai $20.5 biliyan, kari kan $20.3 biliyan da ya mallaka a watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan masu kudin Afrika sune:

Aliko Dangote

Ya mallaki $20.5 biliyan. Shine na 96 a jerin bayan ya sani karin $959 miliyan tun daga farkon shekarar nan.

Dukiyar Dangote tana cigaba da tumbatsa saboda karuwar farashin simintin Dangote. Shi ne kamfanin da yafi kowanne kamfani samar da siminti a nahiyar Afrika inda suka samar da kudin shiga har N891.7 biliyan, kusan $2.5 biliyan a 2019.

Kamfanin Dangote ya mayar da hankali wurin samar da sikari, gishiri, takin zamani da abinci.

Johann Rupert da iyalansa

Rupert shine na biyu a jerin masu arzikin Afrika kuma na 222 a nan duniya inda ya mallaki dukiya mai kimar $8.96 biliyan.

Business Insider ta rahoto cewa shi ne daya daga cikin sanannen biloniyan Afrika ta kudu mai hannayen jari a kamfanonin kasashen ketare ta Remgro.

Kara karanta wannan

Arzikin nufin Allah: Kudi sun karu, Dangote ya zama na 65 a jerin masu kudin duniya

Yana juya kudinsa ne a fannin harkar kudade, kiwon lafiya, abubuwan ci, masana'antu, ababen more rayuwa, sadarwa da masana'antun wasanni.

Nicky Oppenheimer

Oppenheimer yana da dukiya da ta kai $8.35 biliyan kuma shine na 240 a cikin jerin biloniyoyi na duniya.

Tunda shekarar nan ta fara, arzikinsa ya kara da sama da $200 miliyan saboda karin darajar kadararsa dake Stockdale da babban birnin Tana, wadanda suka wuce matsayin Regina dake Egypt, kamfani na biyu mafi girma a samar da taliya da fulawa.

Native Kirsh daga Afrika ta kudu

Shi ne mutum mafi arziki na 266 a duniya wanda kimarsa ta kai $7.67 biliyan a makonni biyu da suka gabata saboda karin darajar Jetro Holdings dake New York kuma ya mallaki manyan kasuwancin abinci a US.

Bloomberg tace kashi 75 na kamfanin shine kashi 61 na jimillar dukiyarsa. Kamfanin yana da darajar $4.8 biliyan.

Nassef Sawiris daga Egypt

Yana da kimar $6.72 kuma shine mutum na 329 a jerin biloniyoyi na duniya.

Kara karanta wannan

Tabdijam: Bidiyon wayar kamfen din Tinubu ta bar 'yan soshiyal midiya baki bude

Yana da kashi 30 na OCI, kamfanin samar da takin zamani na Netherlands wanda aka kafa da hadin guiwar kasuwancin iyalinsa, Orascom Construction.

Sauran kadarorinsa sun hada da kashi 6 na kamfanin kayan wasanni, Adidas da kuma hannayen jari da LafargeHolcim, babban kamfanin samar da siminti na duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel