Tirkashi: Mutumin da ya yi Hajjinsa a Kano ya magantu, ya bayyana dalilansa

Tirkashi: Mutumin da ya yi Hajjinsa a Kano ya magantu, ya bayyana dalilansa

  • Bakanon da ya kudiri aikin hajji a jihar Kano ya magantu da manema labarai kan dalilinsa na daura harami a Kano
  • Ya bayyana haka ne a kwana biyun Sallah, inda ya shaida irin kuncin da ya shiga da kuma yadda ya magance matsalolinsa
  • A bangare guda, ya rusa aikin nasa, ya kuma ce ya yi ne domin nishadantar da 'yan uwansa da suka rasa jirgi

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kano - Jim kadan bayan da alhazai a kasar Saudiyya suka ida aikin Hajjin bana, wani da ya yi na a jihar Kano ya magantu kan dalilin da yasa ya sauke farali a birnin na Kano.

A ranar Alhamis din da ta gabata bayan tashin jirgin karshe na alhazan Najeriya, rahotanni sun karade kasar nan cewa an samu wani fusataccen da ya daura haramar aikin hajji a filin horar da alhazai da ke Kano.

Dalilin da yasa Bakano ya yi Hajji a Kano
Tirkashi: Mutumin da ya yi Hajjinsa a Kano ya magantu, ya bayyana dalilansa | Hoto: aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

An ga Mallam Jibrin Abdu sanye da harami, inda ya ce shi kam a nan Najeriya zai yi hajjinsa, lamarin da ya dauki hankulan jama'ar Najeriya a makon.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ga Mallam Jibrin Abdu sanye da harami, inda ya ce shi kam a nan Najeriya zai yi hajjinsa, lamarin da ya dauki hankulan jama'ar Najeriya a makon.

Abdu, wanda dan asalin karamar hukumar Gezawa ne a jihar Kano, ya zanta da jaridar Aminiya, inda ya bayyana dalilinsa na aikata Hajjin a Najeriya.

Ya shaida cewa, ba da wata manufa ya yi hakan ba face don ya wanke damuwar da ya shiga na rasa jirgi duk da cewa kuwa ya biya kudaden sa.

A cewarsa, domin rage zafi, hakan ya sa ya kulla alwala ya tashi domin yin Sallah da kuma zagayawa kamar dai na aikin Hajji.

Jaridar ta naqalto Jibrin Abdu na cewa:

“Yadda hankulan jama’a suka tashi, kowa na cikin damuwa, ana ta kuka ana ta tsinuwa ya sa na yi wannan shigar don jan hankulan mutane ko sa samu sauki.
“Alhamdulillah, hakan ya yi tasiri kwarai da gaske domin na ga mutanen da ke kuka sun koma dariya.”

Aikin Hajji a Kano ba ingantacce bane

A bangare guda, da kansa ya rusa aikin Hajjin nasa, inda ya ce bai kammala saboda aikin Hajji a Kano bai da inganci ko asali.

A kalaman sa, lokacin da yake mai da komai ga Allah:

“Allah Bai kira mu ba. Wadanda suka samu damar zuwa kuma Allah Ya dawo da su cikin koshin lafiya, Ya kai mu wata shekarar cikin koshin lafiya.”

Dirama yayin da Wani mutumi ya fara gudanar da aikin Hajji a sansanin Alhazai na Kano

A baya kunji cewa, wani abu kamar almara ya faru a Kano ranar Alhamis yayin da wani maniyyaci da bai samu shiga rukunin ƙarshe da jirgi ya ɗiba zuwa ƙasa mai tsarki ba, ya ayyana cewa zai gudanar da Hajjinsa cikakke a sansanin Alhazai.

Malam Jibrin Abdu daga garin Gezawa ya zama abun kallo bayan an gan shi cikin shigar farin Harami kuma ya bayyana cewa tuni ya fara aikin Hajjinsa a sansanin.

Daily Trust ta ruwaito Mutumin ya ce: "Na fara tun tuni tunda muna da kayan aiki baki ɗaya anan kuma tabbas zan dawo na ƙarisa aikin Hajji na cikakke. Na san yadda ake yi domin wannan ba shi ne karon farko ba kuma ba zai zama na karshe ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel