Zargin Cire Sassan Mutum: Jami'ar Lincoln A Birtaniya Ta Yi Hannun Riga Da Ekweremadu

Zargin Cire Sassan Mutum: Jami'ar Lincoln A Birtaniya Ta Yi Hannun Riga Da Ekweremadu

  • Jami'ar Lincoln da ke Birtaniya ta dakatar da Sanata Ike Ekweremadu da cigaba da aiki a matsayin farfesa mai ziyara
  • Hakan na zuwa ne sakamakon zargin da mahukunta a Birtaniya ke masa da matarsa Beatrice na safarar yaro dan shekara 15 don cire kodarsa
  • Mai magana da yawun jami'ar ya bayyana cewa duk da yan sanda ba su kammala bincike ba, jami'ar ba ta bukatar Ekweremadu ya cigaba da aikin farfesa mai ziyarar don girman zargin da ake masa

Jami'ar Lincoln ta hana tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu cigaba da aikinsa a matsayin farfesa mai kai ziyara bayan zarginsa da safarar yaro dan shekara 15 zuwa Birtaniya don cire kodarsa, rahoton Channels Television.

A halin yanzu, Mr Ekweremadu da matarsa, Beatrice suna tsare hannun hukuma a Birtaniyan kan zargin, suna jiran shari'a a ranar 7 ga watan Yuli.

Kara karanta wannan

An tono shekarun yaron da Sanata Ekweremadu suka kai Ingila domin cire masa koda

Ekweremadu Da Matarsa.
Zargin Cire Sassan Mutum: Jami'ar Lincoln A Birtaniya Ta Yi Hannun Riga Da Ekweremadu. Hoto: @ChannelsTV.
Asali: Twitter

Dukkansu biyu sun musanta zargin da ake musu na safarar mutum.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ekweremadu ya shafe kimanin makonni biyu a Birtaniya kafin aka kama shi, bayan ya gana da yan Najeriya mazauna Birtaniya a Lincoln kimanin kwanaki 10 da suka gabata.

Ya kasance yana koyarwa a matsayin farfesa na 'corporate and international linkages' a Jami'ar Lincoln.

Amma, a cewar mai magana da yawun jami'ar da ya yi magana da wata jarida ta Birtaniya, Daily Mail, Jami'ar ta ce ta dakatar da shi daga duk wani aiki a hukumance.

"Galibi, farfesa mai ziyara, tamkar irin wannan, ba zama ya ke a jami'ar ba, kuma ba a biyansa albashi kawai shawarwari ya ke bada wa," a cewar kakakin jami'ar.
"Mun damu matuka da yanayin zargin amma duba da cewa yan sanda ba su kammala bincike ba, ba za mu ce wani abu fiye da haka ba.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya jajantawa Sanatan da aka kama da zargin safarar sassan jikin mutum a Birtaniya

"Yayin da ake bincike, mutumin ba zai cigaba da aiki a matsayin farfesa mai ziyara ba a Lincoln."

Zargin Cire Sassan Jikin Mutum: Sanatoci Suna 'Tare Da Ekweremadu', In Ji Smart Adeyemi

A wani rahoton, dan majalisar tarayyar Najeriya, Sanata Smart Adeyemi ya ce sanatoci ba za su yi watsi da Sanata Ike Ekweremadu ba kuma wasu cikinsu na kokarin tuntubarsa.

Yana martani ne kan zargin cire sassan jikin mutum da aka yi wa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan.

Yan sanda a Birtaniya, a ranar Alhamis sun kama tare da gurfanar da Sanata Ekweremadu da matarsa kan zarginsu da hadin baki don kawo yaro Birtaniya da nufin cire sassan jikinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel