Wata sabuwa: Majalisar dinkin duniya na duba yiwuwar haramtawa maza masu mace 1 karin aure

Wata sabuwa: Majalisar dinkin duniya na duba yiwuwar haramtawa maza masu mace 1 karin aure

  • Domin kare yancin mata a duniya, Majalisar dinkin duniya na duba yiwuwar haramtawa maza auren mace sama da guda daya
  • Hukumomin kare hakkin dan adam da mai yaki da cin zarafin mata ne suka gabatar da wannan bukata a gaban majalisar domin kwatarwa mata yancinsu
  • Wani bincike da aka gudanar ya dai nuna cewa an fi samun yawan auran mace fiye da guda daya a tsakanin Musulman nahiyar Afrika

Rahotanni sun kawo cewa hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya da takwararta mai yaki da cin zarafin mata na neman hana zama auren mace sama da guda daya.

A cewar hukumomin, sun bukaci daukar wannan matakin ne saboda abin da suka kira da kare yancin mata a fadin duniya.

RFI ta rahoto cewa wani bincike da Cibiyar Pew da ke kasar Amurka ta gudanar a kasahe 130 da wasu yankuna, alkaluma sun nuna kaso biyu cikin dari ne kacal ke zama a gidajen da ake da mata sama da guda daya a duniya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Malaysia za ta daure ko cin tarar 'yan kasa da ke cin abinci da rana a Ramadan

Wata sabuwa: Majalisar dinkin duniya na duba yiwuwar haramtawa maza masu mace 1 karin aure
Wata sabuwa: Majalisar dinkin duniya na duba yiwuwar haramtawa maza masu mace 1 karin aure Hoto: RFI
Asali: UGC

Rahoton ya bayyana cewa an haramta auran mace sama da guda daya a sassan duniya da dama, ciki harda nahiyar Turai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai kuma, rahoton ya nuna cewa an hallata shi a kasashen Gabas ta Tsakiya, Asia da kuma yankunan Afrika.

Bincike ya nuna cewa an fi samun auran mata da yawa a yankin Afrika da ke kudu da Sahara, inda kaso 11 cikin dari na al’ummar yankin suka fito daga gidaje da ake auren mata da yawa.

Har ila yau, binciken ya nuna cewa kaso 36 na al’ummar Burkina Faso na da mata sama da daya, yayin da ake da kaso 34 a Mali, sai kaso 30 a Gambia sannan kaso 29 a Jamhuriyar Nijar.

Alkaluma sun kuma nuna cewa kaso 28 na al’ummar Najeriya na da mace sama da daya, yayin da Guinea ke da kaso 26.

Kara karanta wannan

Kudi na magana: Dan kwallon Najeriya Ahmad Musa ya ginawa talakawa katafariyar makaranta a Jos

Binciken ya nuna cewar an fi samun auran mace sama da guda a tsakanin al’ummar Musulman Afirka, sabanin yadda ake samu daga mabiya addinin kiristanci.

Matashi dan shekara 25 zai auri sa'ar kakarsa yar shekara 85

A wani labari na daban, mun ji cewa duk da banbancin shekaru 60 dake tsakaninsu, wani matashi dan shekara 25 ya shiga rumbun soyayya da wata tsohuwa yar shekara 85 mai suna Thereza.

Thereza da Muyiwa na shirin auren juna duk da 'yayan masoyiyarsa da abokinsa sun nuna rashin amincewarsu.

Muyiwa ya bayyanawa Afrimax a wata hira cewa ya bar kasarsa Congo ne don karatu a jami'a. Sai ya kama gidan haya hannun Thereza tare da abokinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel