Matashi dan shekara 25 zai auri sa'ar kakarsa yar shekara 85

Matashi dan shekara 25 zai auri sa'ar kakarsa yar shekara 85

  • Wani matashi dan shekara 25 mai suna Muyiwa na shirin angwancewa da masoyiyarsa yar shekara 85
  • Matashin ya ce yadda tsohuwar take kula da shi ya sa yace kawai yana sonta kuma yana son aurenta
  • Tsohuwar nada 'yaya takwas, jikoki ashirin kuma suna zama a gidansa da Muyiwa da abokansa ke zama

Duk da banbancin shekaru 60 dake tsakaninsu, wani matashi dan shekara 25 ya shiga rumbun soyayya da wata tsohuwa yar shekara 85 mai suna Thereza.

Thereza da Muyiwa na shirin auren juna duk da 'yayan masoyiyarsa da abokinsa sun nuna rashin amincewarsu.

Matashi dan shekara 25
Matashi dan shekara 25 zai auri sa'ar kakarsa yar shekara 85 Hoto: YouTube/Afrimax
Asali: UGC

Yadda Muyiwa ya hadu da Thereza

Kara karanta wannan

Gabansa ba ya aiki: Tsohuwa mai shekaru 54 ta nemi saki a gaban kotu

Muyiwa ya bayyanawa Afrimax a wata hira cewa ya bar kasarsa Congo ne don karatu a jami'a. Sai ya kama gidan haya hannun Thereza tare da abokinsa.

Muyiwa yace a baya ya yi soyayya da yan mata bai ji da dadi ba, amma Thereza daban take kuma yana tsoron kada ta mutu da wuri.

Yace:

"Na tuna ranar wata Juma'a lokacin da abokin zama na baya nan, ina jin yunwa kuma ba mu da abinci. Na jigatu. Kwatsam sai tsohuwar ta kawo min abinci."
"Yadda ta kula da ni yasa na fara son ta. Duk da cewa tsohuwa ce kuma ta kai shekarun kakata, amma ina sonta."

Muyiwa ya yi kira ga masu zaginsa su rabu da shi, abinda yake so kenan.

"Wannan ne zabi na, kuma shine farin ciki na."

Sun kusa shiga daga ciki

Thereza ta bayyana cewa tana son Muyiwa sosai kamar yadda yake sonta. Ta ce shirye take su shiga da ciki.

Kara karanta wannan

Wajibi ne APC ta lashe zabe a 2023 saboda ban taba rashin nasara ba, Abdullahi Adamu

Tace:

"Shekaru na 85. Inada yara 8 da jikoki 20. Idan aka lura da shekarun saurayina, kusan sa'in jikana na biyar ne. Yana so na kuma ina son sa. Shirye nike in aure sa."

Kalli bidiyon:

Tsokacin yan Najeriya

Abdurrahman Ahmad yace:

"Shegiya duniya yaga kudi yana jiran Allah ya kar giwa kasa ya samu yarinya mai jini ajika yayi huff da jita."

Khaleepha M Salees Sumaila yace:

"Batayi tsufaba tunda tanada kudi, awannan yanayin kowa yasamu wannan damar bazayyi wasada itaba, dukkuma wanda yakushewa wannan matashin to hassada yake masa."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel