Ramadan 2022: Sunayen limaman da za su jagoranci Tarawih da Tahajjud a Masjid Al Haram

Ramadan 2022: Sunayen limaman da za su jagoranci Tarawih da Tahajjud a Masjid Al Haram

  • Hukumomin kasar Saudi Arabia sun saki sunayen limaman da za su jagoranci sallolin Tarawihi da Tahajjud a masallacin Harami dake Makkah na watan Ramadanan shekarar nan
  • Sai dai, Haramain sun saki bayani game da raba jagorancin salloli ko lokutan da limaman zasu jagoranci sallar Tarawihi a watan nan mai alfarma
  • A yanzu, babu bukatar jamaa da za su yi sallar Tarawihi a masallacin Annabi da su bi dokar dakile korona, sai dai zasu gabatar da alamar tabbatar da suna da cikakkiyar lafiya a manhajar Tawakkalna

Hukumomin kasar Saudiyya sun saki sunayen limaman da za su jagoranci sallolin Tarawihi da Tahajjud a masallacin Harami dake Makkah na watan Ramadanan wannan shekarar. Sakin jerin sunayen limaman yazo ne ta shafin

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kutsa har cikin gida, sun bindige Shahararren ɗan kasuwa har Lahira

a ranar 23 ga watan Maris.

Jerin sunayen limaman da zasu jagoranci sallar Tarawihi da Tahajjud a masallacin Harami sun hada da.

Ramadan 2022: Sunayen limaman da za su jagoranci Tarawih da Tahajjud a Masjid Al Haram
Ramadan 2022: Sunayen limaman da za su jagoranci Tarawih da Tahajjud a Masjid Al Haram Hoto daga theislamicinformation.com
Asali: UGC

Ga sunayen limamai shida da za su jagoranci sallolin Tarawihi da Tahajjud a masallacin Harami cikin watan Ramadanan 2022, wanda za a fara a farkon watan Afrilu.

  1. Sheikh Abdullah Awad Al Juhany
  2. Sheikh Abdur Rahman Al Sudais
  3. Sheikh Saud Al Shuraim
  4. Sheikh Maher Al Muaiqly
  5. Sheikh Yasir Al Dawsary
  6. Sheikh Bandar Baleelah.

Duba da sunayen limaman da aka saki, za'a iya cewa babu bakon limamin da aka naɗa a wannan shekarar.

Sai dai, shafin Haramain sharifain ya saki bayani game da raba jagorancin salloli ko lokutan da limaman za su jagoranci sallar Tarawihi a watan Ramadanan, kamar haka.

Dama, Musulmai a faɗin duniya sun dade suna matsanancin farin cikin samun labari mai dadi game da yadda za a gudanar da sallolin Tarawihi a masallacin Harami da masallacin Annabi a watan Ramadanan wannan shekarar a cike.

Kara karanta wannan

Buhari ya bada izinin fitar da kudi N14bn don baiwa marasa digiri 500,000 aikin N-Power, Sadiya

Shugabannin lamurran masallatan guda biyu sun sanarwa ƴan gari da baƙi daga ƙasashen duniya yadda za a bar su suyi sallar Tarawihi a masallatan guda biyu.

Musulman fadin duniya sun ji daɗin jin wannan labarin duba da yadda mutane da dama basu samu damar yin sallar Tarawihi na shekarar 2021 a masallacin Harami ba, wanda mutane ƙalilan aka bawa damar yin sallar, wadanda suka haɗa da shuwagabannin masallacin Haramin tare da mazauna kasar, saboda a lokacin ne gwamnati ta tilasta kulle gami da haramtawa baƙi daga wasu kasashen shiga masallacin domin gudun yaɗuwar cutar Korona.

A halin yanzu, ba a bukatar masu bautan da zasu halarci sallar Tarawihi a masallacin Annabi da su bi dokar korona.

Kawai ana bukatar su gabatar da alamar da zai tabbatar da suna da cikakkiyar lafiya a manhajar Tawakkalna kafin su shiga masallatan guda biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel