An sake zaben Finland a matsayin kasa mafi farin ciki a duniya, Najeriya ce ta 118, Afghanistan ce mafi ƙunci

An sake zaben Finland a matsayin kasa mafi farin ciki a duniya, Najeriya ce ta 118, Afghanistan ce mafi ƙunci

  • Yanzu haka Finland ce kasar da ta fi ko wacce farin ciki a duniya kusan shekaru 5 kenan kamar yadda binciken majalisar dinkin duniya ya nuna
  • Bisa yadda manuniyar ta nuna, kasar Afghanistan ce kasar da take fama da kunci da rashin annashuwa daga ita sai kasar Lebanon
  • Kasar Serbia, Bulgaria da Romania ma suna cikin walwala mai yawa yayin da jerin da aka saki a ranar Juma’a ya nuna yadda har kasar Venezuela take cikin kunci tare da Najeriya

Finland ita ce kasar da ta fi ko wacce kasa farin ciki kamar yadda rahoton UN ta nuna, ta kasance a wannan matakin na tsawon shekaru 5, yayin da kasar Afghanistan da Lebanon suka kasance kasashen da suka fi ko wanne bakin ciki da kunci a duniya, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yadda Buhari da Gwamnoni suka karbo bashin Naira Tiriliyan 6.64tr a cikin shekara daya

Serbia, Bulgaria da Romania sun yi sama a jerin wanda hakan na nuna yadda kasashen ke cikin walwala. Sai dai wadanda manuniyar ta nuna a kasa kamar yadda jerin da aka saki ranar Juma’a ya nuna, yayin da Lebanon, Venezuela da Afghanistan suka yi kasa a farin ciki.

An sake zaben Finland a matsayin kasa mafi farin ciki a duniya, Najeriya ce ta 118, Afghanistan ce mafi ƙunci
Farin cikin 'yan Najeriya ya sake raguwa, Finland ta sake zama kasa mafi farin ciki a duniya shekara 5 jere. Hoto: Hoto: Pius Utomi Ekpei Read
Asali: Getty Images

A jerin, Najeriya ta zama kasa ta 118 wacce take cikin kasashe 17 da ke kasan jerin, inda Libya ta zama kasa ta farko a nahiyar Afirka.

Kasar Afirka ta Kudu ta zama ta 91, Gambia ta zo a ta 93, Algeria ta 96, Liberia ta 97, Congo ta 99, Morocco 100, Mozambique 101 sannan Kamaru ta zama ta 102.

Kasashe irin su Senegal da Nijar sun zarce Najeriya farin ciki

A can saman Najeriya akwai Senegal wacce ta zama ta 103, Nijar 104, Gabon 106, Guinea 109, Burkina Faso 113, Benin 115, Comoros 116 da Uganda 117.

Kara karanta wannan

Kun kyauta: Amurka ta taya EFCC murnar kama mai laifin da FBI ta dade tana nema

Daga nan The Punch ta nuna yadda Najeriya ta zo a ta 118, Kenya 119, Tunisia 120, Mali 123, Nambia 124, Madagascar 128, Egypt 129 da Chad ta 130.

Yanzu haka kasar Lebanon tana fama da tabarbarewar tattalin arziki wanda hakan yasa ta sauka ta koma kusa da karshen jerin inda ta zama ta 146, karkashin Zimbabwe.

Rikicin Afghanistan ya sanya ta a can kasa tun bayan Taliban ta amshi mulki a watan Augustan da ya gabata.

A kiyasin UNICEF, yara miliyan daya za su iya mutuwa a Afghanistan idan basu samu tallafi ba

UNICEF ta kiyasta cewa yara miliyan daya ne wadanda basu kai shekaru 5 da haihuwa ba zasu iya mutuwa a cikin wannan lokacin sanyin in har ba a tallafa musu ba.

Wanda ya shirya jerin, Jan-Emmanuel De Neve ya ce:

“Wannan jerin ya nuna irin yadda tattalin arzikin kasashe ya tabarbarewa saboda yaki wanda ya janyo illa ga mazauna kasashen.”

Kara karanta wannan

Abin al'ajabi: Labarin Baturiyar da ta shekara 30 tana karantar da Hausa a Najeriya

An kai shekaru 10 ana yin rahoto akan farin cikin duniya, kuma ana kawo jerin farin cikin da ke kasashe ne bayan duba akan tattalin arziki da kuma yanayin rayuwar da mazauna kasar suke ciki.

Ma’aunin farin ciki yana farawa ne daga 0 zuwa 10, bayan tattaro bayanan kasashe na tsawon shekaru 3. An yi wancan jerin ne kafin Rasha ta afka Ukraine.

Kasashen Europe na arewa sun kara mamaye saman jerin yayin da Danes take bayan Finns, daga nan sai Icelandic, Swiss sannan Dutch.

Amurka ta daga da lambobi 3 ta zama ta 16 inda ta koma saman Burtaniya, yayin da Faransa ta zama ta 20.

A bangaren annashuwa kuwa, Gallup ta yi can saman gaba daya kasashe. Ma’aunin farin cikin yana bukatar gwajin GDP, walwala, tallafi da kuma rashawa a kasashe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel