Ta kare wa Putin: Shugaban Rasha na neman sojojin da za su taya shi yaki da Ukraine

Ta kare wa Putin: Shugaban Rasha na neman sojojin da za su taya shi yaki da Ukraine

  • Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa Rasha na shirin daukar mayaka daga kasashen waje yayin da take kara kaimi kan yakar Ukraine
  • A cewar kakakin ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon, John Kirby, Rasha na kokarin daukar 'yan Siriya ne musamman don ci gaba da yaki
  • A halin da ake ciki kuma, Rasha ta aike da sojoji sama da 150,000 zuwa cikin Ukraine a ci gaba da hare-haren da take kai wa

Washington, Amurka - Rahotanni daga kasashen waje sun ce, shugaba Vladimir Putin na neman daukar mayakan kasashen waje da za su yi yaki da Ukraine a madadin sojojin Rasha.

Ma'aikatar Tsaro ta Amurka ce ta bayyana hakan. Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce Putin na neman daukar mayakan ne musamman daga Siriya.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Rukunin farko na yan Najeriya mazauna Ukraine sun iso Abuja

Kakakin Pentagon John Kirby wanda ya bayyana hakan ga CNN ya ce akwai alamun da ke tabbatar da rahoton.

Shugaba Putin ya nemi sojojin haya daga kasashen waje
Ta kare wa Putin: Shugaban Rasha na neman sojojin da za su taya shi yaki da Ukraine | Hoto: aljazeera.com
Asali: UGC

Putin dama ya riga ya tura sama da sojojin Rasha 150,000 cikin Ukraine. A cewar rahotanni, dakarun Ukraine sun tari sojojin na Rasha kana sun yi arangama.

A cewar jaridar Wall Street, jami'an Amurka sun ce Rasha a cikin 'yan kwanakin nan ta dauki mayaka daga Siriya, da nufin za su taimaka wajen karbe babban birnin kasar Ukraine; Kyiv da sauran garuruwa.

Wani jami'i ya shaida wa jaridar cewa, tuni wasu mayaka suka je Rasha suna shirin shiga yakin na Rasha da Ukraine, ko da yake ba a bayyana adadin mayakan da aka dauka ba.

A cewar wata wallafa ta Deir Ezzor, Siriya, Rasha ta ba sojin na sa kai daga kasar Siriya dalar Amurka $200 zuwa dala 300 “domin su je Ukraine su yi aikin gadi” na tsawon watanni shida a lokaci guda.

Kara karanta wannan

Yana Da Katafaren Fada A Cikin Daji: Abubuwa 4 Masu Mamaki Game Da Shugaban Rasha Vladimir Putin

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya nakalto Ramzan Kadyrov shugaban jamhuriyar Chechnya kuma dan tsagin shugaban Rasha Vladimir Putin na cewa, an kuma tura dakarun Checheniya zuwa kasar ta Ukraine.

Akwai matsala: Ba za mu bari 'yan Najeriya su tafi Ukraine yaki ba, gwamnatin Buhari

A wani labarin na daban, wani rahoton jaridar Punch ya ce, Gwamnatin Tarayya ta bayyana rashin amincewarta da ci gaba da yi wa ‘yan Najeriya rajistar shiga yakin Ukraine domin tinkarar sojojin Rasha da ke mamaye da kasar.

Idan baku manta ba, sama da ‘yan Najeriya 150 ne suka nuna sha'awar shiga yakin Ukraine, shugaban kasar , Volodymyr Zelensky, ya bukaci 'yan sa kai daga kasashen duniya su shiga yakin domin tinkarar abokiyar hamayyarta; Rasha.

Sai dai da take mayar da martani a wata sanarwa a ranar Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen tarayya, Francisca Omayuli, ta ce gwamnatin tarayya ba za ta amince da daukar 'yan Najeriya a tura su Ukraine ba.

Kara karanta wannan

Mun yi rashin Sojojimu kusan 500, an jikkata kimanin 1600 a Ukraine: Kasar Rasha

Asali: Legit.ng

Online view pixel