Yana Da Katafaren Fada A Cikin Daji: Abubuwa 4 Masu Mamaki Game Da Shugaban Rasha Vladimir Putin

Yana Da Katafaren Fada A Cikin Daji: Abubuwa 4 Masu Mamaki Game Da Shugaban Rasha Vladimir Putin

Ba za a yi kuskure ba idan aka ce Shugaban Rasha Vladmir Vladimirovich Putin shine mutumin da aka fi magana a kansa a duniya a yanzu tun bayan da kasarsa ta kutsa Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu.

Duk da takunkumin da wasu manyan kasashen duniya da suka cigaba suka saka masa da kuma Allah wadai da kasashen duniya da dama suka yi, Shugaban dan shekara 70 ya cigaba da kiran abin da ya ke yi 'aikin kawo zaman lafiya' a Ukraine.

Yana Da Fada A Cikin Daji: Abubuwa 4 Masu Mamaki Game Da Shugaban Rasha Vladimir Putin
Abubuwa 4 Masu Mamaki Game Da Shugaban Rasha Vladimir Putin. Photo Credit: MikhailSvetlov, Wikimedia Commons
Asali: Getty Images

Legit.ng ta yi duba kan wasu muhimman abubuwa guda hudu game da mutumin da ya yi sanadin mutuwar daruruwan sojojin Rasha da Ukraine; ya janyo wasu da dama suka rasa muhallansu, yan Ukraine da yan wasu kasashen.

1. Putin yana da katafaren fada a cikin daji

Kara karanta wannan

ICPC Ta Kama Wani Jami'in Rundunar Tsaro Ta NSCDC Da Zamba Cikin Aminci

Duk da birane da suke a duniya, Putin ya zabi daji domin gina katafaren fadarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon jami'in tattara bayan sirrin yana da wani katafaren gida da ake kira Fadar Putin da ke kusa da Black Sea a Krasnodar Krai, Rasha, History Hit ta rahoto.

A gidan mai girman 18,000m2, akwai wurin saukar jirgi mai saukan ungulu, coci, gidan baki, gidan man fetur, gada mai tsawon mita 80, gida na musamman da hanyar kasa da ta ratsa cikin duwatsu.

A cikin gidan akwai kayayakin alatu da jin dadi kamar wurin wanka na musamman (spa), shaguna, dakin ajiya, dakin karatu, wurin sauraron waka, wurin shan lemun kwalba da giya, sinima da dakin baki.

2. Putin ya girma cikin talauci ne

A lokacin da ya ke tasowa, Shugaban na Rasha ya girma ne cikin talauci.

Kara karanta wannan

Dala 500k/N220m: Tulin miliyoyin da dan Najeriya ya kai banki zai ajiye ya girgiza jama'a

A cewar History Hit, mahaifiyar Putin tana aikin sharar titi da wanke kayan aiki a dakunan bincike na kimiyya yayin da mahaifinsa aiki ya ke a kamfanoni, bayan yakin duniya na II.

Putin da iyayensa sun zauna ne a unguwa ta talakawa inda akwai beraye da dama.

3. Putin yana kaunar tawagar mawaka mai suna The Beatles

Shahararrun mawaka na Burtaniya, The Beatles, suna da masoya a fadin duniya kuma Putin na daya daga cikinsu.

An gano irin wakokin da Putin ya ke kauna ne bayan wata tataunawa da ya yi da mai daukan hoto dan kasar Birtaniya a 2007.

A shekarar, Mujalar Time Magazine ne ta aika mai daukan hoton, mai suna Platon ya dauki hoton Putin, domin wallafa hotonsa a mujallarsu a matsayin 'gwarzon shekara'.

A farkon tattaunawarsu, Platon ya ce yana kaunar Beatles kuma ya tambayi Putin ko shima yana son su kamar yadda wani rahoton History Hit ya nuna.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Ceto ‘Yan Najeriya Daga Yunwa Inji Ministan Buhari

"Ina kaunar Beatles!," aka ruwaito Putin ya ce, ya kara da cewa wakarsu mai lakabin Yesterday ce ya fi kauna.

4. Putin yana kaunar dabobbi

An rahoto cewa Putin yana da karnuka da yawa da ke kiwo don sha'awa. Ya kan yawaita daukan hoto tare da dabobin.

A baya, ya yi kokarin ganin an yi dokoki da za su tabbatar an rika kyautata wa dabobbi har da dokar hana kawo dabobi cikin shaguna da wurin cin abinci.

Ukraine: Ba Bu Abin Da Zai Faru Da 'Yan Najeriya, Rasha Ta Faɗa Wa FG

A wani labarin, Jakadan kasar Rasha a Najeriya, Alexei Shebarshin, ya tabbatar wa gwamnatin tarayya cewa ‘yan Najeriya baza su cutu ba a rikicin da ke ta ballewa tsakanin kasar Rasha da Ukraine, The Punch ta ruwaito.

Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, wanda ya samu damar ganawar sirri da jakadan ya shaida wa Shebarshin cewa Najeriya kawar Rasha ce.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki na gaban goshin Atiku a jihar gwamnan PDP mai adawa da Atiku

A cewar Onyeama, yayin tattaunawa da Shebarshin ya sanar da shi cewa Najeriya baza ta lamunci cin zarafin kasa da kasa ba daga wata kasar da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya, kasar da ke da jakada a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel