Rudani: An tsinci gawar saurayi da Budurwa a cikin dankareriyar Mota, ana zargin suna saduwa suka mutu

Rudani: An tsinci gawar saurayi da Budurwa a cikin dankareriyar Mota, ana zargin suna saduwa suka mutu

  • Mutane sun gano gawar mace da namiji da ake zargin masoya ne a cikin motar Sienna Toyota a jihar Ogun
  • Lamarin dai ya tada hankulan mutanen yankin, sun bayyana cewa kwanan motar biyu a wurin ba'a motsa ta ba
  • Kakakin yan sanda na jihar ya musanta raɗe-raɗin cewa nutanen na tsaka da saduwa suka mutu

Ogun - Cece-kuce ya yi yawa kan musabbabin mutuwar wasu Masoya a cikin Mota a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan ranar Laraba.

A cewar wani shaidan gani da ido, Masoyan sun rasa rayukansu ne yayin da suke tsaka da saduwa a cikin motar Toyota Sienna a yankin NASFAT kusa da garin Mowe-Ibafo dake kan babbar hanyar.

Sai dai jaridar Punch ta rahoto cewa hukumar yan sandan jihar Ogun ta musanta cewa mutanen sun mutu ne suna cikin jima'i.

Kara karanta wannan

Wani bawan Allah ya daba wa dan Acaba makami har lahira kan ya buge masa Kare a Gombe

An tsinci gawa a Mota
Rudani: An tsinci gawar saurayi da Budurwa a cikin dankareriyar Mota, ana zargin suna saduwa suka mutu Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Gawarwakin masoyan sun tada hankulan jama'a, yayin da masu wucewa ke tsayawa suna ɗaukar hotuna da bidiyon wurin da abun ya faru.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ya aka gano cewa sun mutu?

Rahoto ya nuna cewa mutanen yankin sun fara zargin akwai matsala bayan Motar ta shafe kwana biyu a wuri ɗaya ba'a motsa ta ba.

A wani Bidiyo da ya watsu, an jiyo wani mutumi na faɗin cewa:

"Motar nan ta shafe kwana biyu a nan wurin. Dan Allah duk wan da ya san mai motar, ya taimaka ya tuntubi Caji Ofis ɗin yan sanda dake Mowe-Ibafo."

Wane matakin yan sanda suka ɗauka?

Da aka tuntubi kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya yi bayanin cewa mutanen biyu da ake zargin masoya ba suna saduwa suka rasu ba kamar yadda mutane ke ta yayatawa.

Kara karanta wannan

Abuja: 'Yan bindiga sun hallaka 'yan mata biyu a hanyarsu ta zuwa biki

The Nation ta rahoto Oyeyemi ya ce:

"Ba suna cikin saduwa suka mutu ba. Tun farko mun samu rahoton Mutumin a caji ofis din Ileja jihar Legas. An kawo mana rahoton ya buga wa budurwarsa wani abu a kai."
"Yayin da yarinyar ta fita hayyacinta, mutumin ya saka ta a Mota ya gudu. Mun samu rahoton ya ɗauki wani maharbi a hanyar zuwa Ogun, daga baya aka ga gawarsu a kusa da NASFAT."

A wani labarin na daban kuma Wani ma'aikacin jami'a ya mutu a cikin ruwan shakatawa a Hotel

Wani ma'aikaci a jami'ar UNICAL ya rasa rayuwarsa yayin da yaje Otal shan iska saboda zafin da ake a birnin Kalaba.

Wata majiya ta bayyana cewa da farko an nemi mutumin an rasa amma wajen karfe 2:00 na dare aka ga gawarsa a saman ruwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262