Babban Magana: A Kawo Min Kan Putin, Zan Bada Tukwicin N415m, Biloniyan Kasar Rasha

Babban Magana: A Kawo Min Kan Putin, Zan Bada Tukwicin N415m, Biloniyan Kasar Rasha

  • Wani dan kasuwa dan kasar Rasha ya ayyana neman Putin ruwa a jallo saboda kai wa Ukraine hari
  • Alex Konanykhin, dan kasuwan ya saka tukwicin Naira miliyan 415 yana mai cewa nauyi ne a kansa ya ga an hukunta Putin
  • Biloniyan ya ce ya fara samun matsaloli da gwamnatin Rasha ne bayan an zarge shi da satan Naira biliyan 3 daga banki

Wani dan kasuwa kuma biloniya dan kasar Rasha ya ayyana neman Shugaba Vladimir Putin ruwa a jallo saboda kai wa Ukraine hari.

Alex Konanykhin, dan kasuwan ya saka tukwicin Naira miliyan 415 yana mai cewa nauyi ne a kansa ya ga an hukunta Putin a cewar The Independent.

Biloniyan Rasha Ya Saka Tukwicin N415m Ga Duk Wanda Ya Kawo Masa Kan Putin
Zan ba wa duk wanda ya kawo min kan Putin N415m, Biloniyan Kasar Rasha. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Mamayar Rasha: Mutane miliyan 1 sun yi gudun hijira a Ukraine cikin mako 1, UNHCR

Nauyi ne da ya rataya a kaina domin adalci

Biloniyan ya yi wannan alkawarin ne cikin wata rubutu da ya wallafa a shafin hada-hada ta LinkedIn kuma ya ce nauyi ne ya rataya a kansa ya dauki matakan taimakawa Ukraine a yayin da ta ke kokarin dakile sojojin Rasha.

A rubutun da ya wallafa, akwai hoton Putin da rubutu mai cewa, Nema ruwa a jallo: Da rai ko a mace. Vladimir Putin saboda yi wa mutane kisan kiyashi.

Tarihinsa da kasar Rasha

Dan kasuwan kansa yana da tarihi mai sarkakiya da gwamnatin kasar Rasha. A shekarar 1996, an kama shi lokacin yana zaune a Amurka bayan jami'an Amurka a Rasha sun ce ya sace N3.3bn daga wani banki.

Daga baya an sake shi bayan alkali ya ce akwai lauje cikin nadi a karar da aka shigar a kansa.

Ukraine: Ba Bu Abin Da Zai Faru Da 'Yan Najeriya, Rasha Ta Faɗa Wa FG

Kara karanta wannan

Mun yi rashin Sojojimu kusan 500, an jikkata kimanin 1600 a Ukraine: Kasar Rasha

A wani labarin, Jakadan kasar Rasha a Najeriya, Alexei Shebarshin, ya tabbatar wa gwamnatin tarayya cewa ‘yan Najeriya baza su cutu ba a rikicin da ke ta ballewa tsakanin kasar Rasha da Ukraine, The Punch ta ruwaito.

Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, wanda ya samu damar ganawar sirri da jakadan ya shaida wa Shebarshin cewa Najeriya kawar Rasha ce.

A cewar Onyeama, yayin tattaunawa da Shebarshin ya sanar da shi cewa Najeriya baza ta lamunci cin zarafin kasa da kasa ba daga wata kasar da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya, kasar da ke da jakada a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel