Mun yi rashin Sojojimu kusan 500, an jikkata kimanin 1600 a Ukraine: Kasar Rasha

Mun yi rashin Sojojimu kusan 500, an jikkata kimanin 1600 a Ukraine: Kasar Rasha

  • Daga karshe, kasar Rasha ta bayyana adadi jami'anta da suka mutu kawo yanzu a yakinta da Ukraine
  • Gwamnatin kasar Ukraine a baya ta sanar da cewa ta hallaka Sojojin Rasha sama da dubu biyu
  • Wannan ya biyo bayan zaben majalisar dinkin duniya UN inda aka bukaci a hukunta kasar Rasha

A karon farko, gwamnatin kasar Rasha ta bayyana adadin dakarun da ta rasa kawo yanzu tun lokacin da Vladimir Putin ya kai fara kai harin kwace Ukraine a makon da ya gabata.

Kakakin hedkwatan tsaron Rasha, Igor Konashenkov, a jawabin da ya saki a tashar Talabijin kasar ya bayyana cewa an hallaka Sojojinsu 498 a Ukraniya.

Yace:

"Sojojinmu dari hudu da casa'in da takwas sun mutu a faggen fama, kuma Sojinmu 1,597 sun jikkata."

Kasar Rasha
Mun yi rashin Sojojimu kusan 500, an jikkata kimanin 1600 a Ukraine: Kasar Rasha
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Najeriya ta shiga cikin sahun kasashen duniya 141 da suka bukaci a hukunta Rasha

Najeriya ta shiga cikin sahun kasashen duniya 141 da suka bukaci a hukunta Rasha

A bangare guda, Najeriya na cikin jerin kasashen duniya 141 da suka kada kuri'a ranar Laraba a majalisar dinkin duniya don a hukunta Rasha bisa hare-haren da take kaiwa kasar Ukraine.

Hakazalika kasashen sun bukaci Rasha ta janye dakarunta daga Ukraine kai tsaye.

Wannan zabe da aka kada ranar Laraba na nufin hukunta Rasha.

Cikin kasashe 193 da suka halarci zaman taron ganganmin majalisar tsaron, mutum 141 su zabi a hukunta Rasha.

Kasashe 35 sun janye daga zabe inda suka ce ba zasu ce hukunta Rasha ba kuma ba zasu ce kada a hukunta Rasha ba.

Kasashe 5 kuwa sun goyi bayan Rasha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel