Mata ta ‘yar bala’i ce, da adda take bi na: Wani mutum ya bukaci kotu ta raba shi da matarsa

Mata ta ‘yar bala’i ce, da adda take bi na: Wani mutum ya bukaci kotu ta raba shi da matarsa

  • Steve Bashorun mai shekaru 61 ya maka matarsa, Oluwaseyi gaban wata kotu da ke Alagbado a Jihar Legas bisa zargin ta da yunkurin halaka shi
  • Steve, mazaunin yankin Ikola ya sanar da kotu cewa shekarun auren su 17 da Oluwaseyi mai shekaru 40, zaman su cike ya ke da tashin-hankali
  • Ya zarge ta da rashin kulawa da yaransu uku sannan tana cin mutuncin mahaifiyar sa kafin ta rasu duk da kokarin sa wurin wadata gida

Legas - Mr Steve Bashorun mai shekaru 61 ya maka matar sa Oluwaseyi, gaban kotun Alagbado da ke Jihar Legas ranar Alhamis bisa zargin ta da yunkurin halaka shi, Vanguard ta ruwaito.

Steve wanda mazaunin yankin Ikola ne ya sanar da yadda suka kwashe shekaru 17 da auren matarsa mai shekaru 40.

Kara karanta wannan

Yadda matar aure ta kashe mijinta, Bello, da tafasasshen ruwa a Ogun

Ya zarge ta da kin kulawa da yaran su uku tare da wulakanta dangin sa musamman mahaifiyarsa, kafin ta rasu.

Mata ta ‘yar bala’i ce, da adda take bi na: Wani mutum ya bukaci kotu ta raba shi da matarsa
Mata ta ‘yar bala’i ce, da adda take bi na: Miji ya nemi kotu ta datse igiyar aurensa da matarsa. Hoto: The Nation
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da bayyana yadda yake kokarin wadata matar sa da abinci amma duk da haka bata girmama shi.

Mijin ya ce matarsa tana fatattakar sa da wuka, adda da tabarya idan sun yi fada

A cewarsa:

“Mata ta ‘yar bala’i ce, tana amfani da adda, wuka da tabarya wurin razana ni. Akwai lokutan da take duba sakwannin waya ta, idan ta hassala sai ta yi yunkurin halaka ni.
“Wani lokacin har tserewa nake yi wurin dayar mata ta in kwashe watanni. A watan Disamban 2021 na dawo gida bayan kwashe watanni 9 a can.
“Bata yi min girki, sai ta ga dama take yi wa yaran mu girki. Rabon da ta yi min girki tun farkon auren mu. Har zagin yayana ta taba yi daga nan yace ba zai kara zuwa gidan mu ba.”

Kara karanta wannan

Kamar a jahiliyya: Uba ya kashe 'ya'yansa tagwaye, za a rataye shi har sai ya mutu

Matar ta musanta zargin

A bangaren Oluwaseyi ta musanta duk wadannan laifukan. Sai dai ta amsa batun rashin yi wa yayan mijin ta girki.

A cewarta ita take yi wa yaran ta girki ta kuma kai su makaranta.

NAN ta ruwaito yadda miji da matar suka ce har yanzu suna son juna. Alkalin kotun, Mr Alli Emmanuel ya shawarce su akan su hada kai don zaman lafiya.

Emmanuel ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 1 ga watan Maris don shirya ma’auratan.

A raba mu, ya ce na cika mugun ci, har rufe kicin yake yi da dare, Firdausi ta yi karar mijinta Haruna a kotu

A wani labarin daban, a ranar Litinin wata Firdausi Sulaiman mai shekaru 23 ta maka mijin ta, Haruna Haruna a gaban kotun musulunci da ke zama a Magajin Gari a Kaduna tana bukatar a raba auren su da shi saboda yadda yake dukanta kamar gangar tashe sakamakon mungun cin abincin ta.

Kara karanta wannan

An maka dalibi mai shekaru 21 a kotu kan tura wa mijin budurwarsa hotunan tsiraicinta

Kamar yadda NewsWireNGR ta bayyana, a korafin da ta yi wa Kotu, Firdausi wacce take zama a Rigasa dake Kaduna ta ce har rufe kicin Haruna yake yi da dare.

Alkalin kotun, Nuhu Falalu, bayan sauraron bangarorin guda biyu, ya dage sauraron shari’ar har sai ranar 4 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel