Rasha ta ragargaza jirgin da yafi kowanne girma a duniya dake kasar Ukraine

Rasha ta ragargaza jirgin da yafi kowanne girma a duniya dake kasar Ukraine

  • Kasar Rasha ta lalata jirgin sama da yafi kowanne girma a duniya na kasar Ukraine mai suna Mriya, wanda ma'anarsa mafarki
  • Kasar Ukraine ta ce Rasha za ta iya lalata Mriya amma mafarkinsu na cigaba da zama kasa mai 'yanci ba zai tarwatsu ba
  • Jirgin saman ya na da tsawon mita wanda ya kai sahun kafa 276 sannan yana iya daukar 250 tonnes(fan 551,000) na kaya

Kasar Rasha ta tarwatsa jirgin da yafi kowanne girma a duniya na kasar Ukraine - Antonov-225 jirgin saman Ukraine, wajen Kyiv a rana ta hudu da sojojin Moscow suka fara kai musu hari, kungiyar Ukrobironprom ta kasar Ukraine ce ta bayyana hakan a ranar Lahadi.

"Mayakan kasar Rasha sun tarwatsa jirgin da kamfanin sufurin jiragen saman Ukraine ke tutiya da shi, AN-225 a filin jirgin Antonov dake Gostomel kusa da Kyiv", kungiyar ta sanar da hakan a wata takarda.

Kara karanta wannan

Shahararren biloniyan Japan, Mikitani, ya gwangwaje Ukraine da tallafin $8.7m

Rasha ta ragargaza jirgin da yafi kowanne girma a duniya dake kasar Ukraine
Rasha ta ragargaza jirgin da yafi kowanne girma a duniya dake kasar Ukraine. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Jirgin ya fita daban daga sauran jirage a fadin duniya, yana da tsawon mita 84 (sawun kafa 276) sannan yana iya daukar 250 tonnes(fan 551,000) na kaya, da gudun a kalla kilomita 850 a cikin awa daya 528 mph).

Daily Trust ta ruwaito cewa, hakan yasa 'yan kasar Ukraine suka sa mai suna "Mriya", ma'ana "Mafarki".

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Wannan shi ne jirgin da yafi kowanne girma a duniya, AN-225 'Mriya" Ministan kula da harkokin waje, Dmytro Kuleba ne ya wallafa hakan a ranar Lahadi ta shafinsa na Twitter.
"Rasha za ta iya lalata mana 'Mriya'. Amma ba za su iya lalata mana mafarki mai karfin ba, kasar Europe mai yanci kuma cike da damokaradiyya. Gaba dai - gaba dai", a cewarsa.
"Filin jirgin Gostomel ya fuskanci matsaloli, tun harin da Rasha ta fara kai musu farmaki," shugaban Vladimir Putin ne ya tabbatar da hakan a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Alkali ya bada umarni hukumar EFCC ta karbe gidan tsohon Gwamnan APC a Abuja

Rundunar sojin Rasha ta bayyana yadda take kokarin kwace manyan makamai.

Makerin makamai, Ukrobironprom ya kiyasta kudin da za a kashe wajen ganin an gyara "Mriya" a sama da $3 biliyan ( euro 2.7 biliyan), sannan za a iya daukar sama da shekaru biyar kafin a gyara.

"Burin mu shi ne, tabbatar da kasar Rasha da tayi gangancin lalata kamfanin sufurin jiragen saman Ukraine ta biya kudin gyaran," a cewar kungiyar.

An kera shi ne a matsayin wani bangare na aikin ilimin kirar jirage da Soviet suka yi, jirgin AN-225 ya fara tashi sama ne a shekarar 1988, Daily Trust ta ruwaito.

Bayan daukar tsawon shekaru ba a hawan jirgi, bayan rushewar Soviet, jirgin da shi kadai ya rage ya fara gwada tashi sama ne a shekarar 2001 a Gostomel, kimanin kilomita 20 daga Kyiv.

Kamfanin jirgin saman Antonov na kasar Ukraine sun dade suna amfani da shi, yayin da aka bukace shi matuka lokacin da cutar Korona ta fara barkewa.

Kara karanta wannan

Rasha ta fara kai hare-hare a Ukraine, ‘Daliban Najeriya 4, 000 sun yi carko-carko

Shahararren biloniyan Japan, Mikitani, ya gwangwaje Ukraine da tallafin $8.7m

A wani labari naa daban, biloniyan kasar Japan, Hiroshi Mickey Mikitani, a ranar Alhamis ya ce zai bai wa gwamnatin kasar Ukraine tallafin $8.7 miliyan inda ya danganta kutsen kasar Rasha da kalubale ga damokaradiyya.

Mamallakin e-commerce din a wasikar da ya aike wa shugaban kasar Ukraine, Volodymr Zelensky ya ce tallafin Yen biliyan dayan zai tafi ne wurin taimakon jama'ar Ukraine wadanda halin tashin hankalin nan ya ritsa dasu, punch ta ruwaito.

Mikitani ya ce ya ziyarci birnin Kyiv a 2019 kuma ya gana da Zelensky.

"Tunani na yana tare da ku da jama'ar Ukraine," Mikitani yace a wasikarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel