Rasha ta fara kai hare-hare a Ukraine, ‘Daliban Najeriya 4, 000 sun yi carko-carko

Rasha ta fara kai hare-hare a Ukraine, ‘Daliban Najeriya 4, 000 sun yi carko-carko

  • Akwai ‘daliban Najeriya da-dama da suke karatu a jami'o'in Ukraine da sun rasa inda za su shiga
  • A halin yanzu yaki ya turnuke tsakanin Rasha da Ukraine a dalilin yunkurin kasar na shiga NATO
  • Mafi yawan kasashe sun dauke ‘ya ‘yansu da ke gabashin Ukraine, ‘Yan Najeriya su na can har yau

Ukraine - ‘Daliban Najeriya da ke kasar Ukraine sun rasa inda za su kansu bayan yaki ya barke tsakanin kasar Rasha da makwabciyarta watau Ukraine.

A wani rahoto da Premium Times ta fitar a ranar Alhamis, 24 ga watan Fubrairu 2022, an ji cewa akwai sama da ‘yan Najeriya 4000 da ke karatu a Ukraine.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bada umarni ga sojojnsa su kai wa dakarun kasar Ukraine hari. Amma ana tsoron cewa harin ya shafi sauran 'yan gari.

Kara karanta wannan

Solomon Dalung ya nemi a yafe masa na yi wa APC kamfe, ya bi Kwankwaso zuwa TMN

CNN ta ce ‘daliban Najeriya da ke makaranta a gabashin Ukraine sun ce kasarsu tayi wasti da su.

Wani ‘dalibin kasar nan da yake Lviv National Medical University, Ukraine mai suna Anjola Philips ya shaidawa ‘yan jarida gwamnati ta yi shiru a kan su.

“Ba mu san abin da yake faruwa ba, mu na ganin sauran kasashe su na aiko jirage, su na dauke mutanensu, ya kamata mu san idan akwai inda za mu taru.”
Ukraine
Kayan yaki a Ukraine Hoto: edition.cnn.com
Asali: UGC

“Ba mu san halin da ake ciki ba, kuma mutane su na tambaya ko ya kamata su koma gida.” - Anjola Philips

Kwanakin baya wannan makarantar koyon aikin likita ta Lviv National Medical University ta fadawa mafi yawan ‘daliban ta cewa za su iya komawa gida.

Kara karanta wannan

Sakamakon zirga-zirgar Buhari: Kasar Ingila ta narka Naira Biliyan 5 domin inganta wuta

Rahoton ya ce wadanda aka kebe su ne ragowar ‘daliban da suke rubuta jarrabawa a halin yanzu.

Mun fara jin tashin makamai

A cewar Felix Ogunlade wani ‘dan Najeriya da yake zaune a babban birnin Kyiv, ya ji karan wasu abubuwa tsakanin karfe 3:00 zuwa 5:00 na safiyar Alhamis.

A wani rahoto da ya fito daga BBC, an fahimci cewa Najeriya da kasar Ghana su na da ‘dalibai da yawa da suke karatu a makarantun da ke yankin Ukraine.

Rasha ta dura Ukraine

Dazu kun ji cewa hotuna da bidiyo sun nuna yadda jiragen kasar Rasha suka kai hari jihohi a kasar Ukraine ranar Alhamis, 24 ga watan Febrairu, 2022.

Kawo yanzu akalla mutum takwas sun hallaka yayinda Rasha ke ikirarin cewa ba tada niyyar kashe farin hula. Hakan barazana ne ga bakin Najeriya a can.

Asali: Legit.ng

Online view pixel