Shahararren biloniyan Japan, Mikitani, ya gwangwaje Ukraine da tallafin $8.7m

Shahararren biloniyan Japan, Mikitani, ya gwangwaje Ukraine da tallafin $8.7m

  • Biloniyan kasar Japan, Hiroshi Mickey Mikitani ya bai wa kasar Ukraine tallafin kudi haar Yen biliyan 1 wanda yayi daidai da $8.7m
  • Yaa aikewa shugaban kasar Ukraine, Volodymr Zalensky, wasika inda yace a yi amfani da kudin wurin tallafawa wadanda kutsen Rasha ya shafa
  • Yaa sanar da cewa, yaa taba ziyartar kasar Ukraine a shekarar 2019 kuma tunaninsa na tare da su, ya yi fatan dawowar zaman lafiya kasar

Biloniyan kasar Japan, Hiroshi Mickey Mikitani, a ranar Alhamis ya ce zai bai wa gwamnatin kasar Ukraine tallafin $8.7 miliyan inda ya danganta kutsen kasar Rasha da kalubale ga damokaradiyya.

Mamallakin e-commerce din a wasikar da ya aike wa shugaban kasar Ukraine, Volodymr Zelensky ya ce tallafin Yen biliyan dayan zai tafi ne wurin taimakon jama'ar Ukraine wadanda halin tashin hankalin nan ya ritsa dasu, punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tambuwal ya gana da daliban jihar Sokoto da ke Ukraine, ya bukaci iyaye da su kwantar da hankalinsu

Shahararren biloniyan Japan, Mikitani, ya gwangwaje Ukraine da tallafin $8.7m
Shahararren biloniyan Japan, Mikitani, ya gwangwaje Ukraine da tallafin $8.7m. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Mikitani ya ce ya ziyarci birnin Kyiv a 2019 kuma ya gana da Zelensky.

"Tunani na yana tare da ku da jama'ar Ukraine," Mikitani yace a wasikarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Na yarda cewa take zaman lafiya da damokaradiyya da aka yi wa Ukraine ba adalci bane kuma kalubale ne ga damokaradiyya.
"Ina fatan Rasha da Ukraine za su shawo kan matsalar da ke tsakaninsu hankali kwance kuma zaman lafiya zai koma Ukraine da gaggawa," ya rubuta.

Kutsen Rasha ya janyo manyan matakai daga manyan damokaradiyyoyi yayin da jama'a da kungiyoyi a fadin duniya suke nemawa kasar Ukraine taimako, punch ta ruwaito.

Gwamnatin Japan ta sanar da matakin da ta dauka kan Moscow wanda ya hada da daskarar da kadarori da daina cinikayya da su.

Dakarun Rasha sun balla babban birnin kasar Ukraine

A wanai labari na daban, dakarun kasar Rasha sun kutsa kai cikin Kyiv, babban birnin kasar Ukraine, a rana ta biyu da fara kaddamar da hare-haren soji cikin kasar.

Kara karanta wannan

Duk shugaban da ya rantse da AlQur'ani kada ya kuskurar yaci amana, Shugaba Buhari

A rahoton da BBC ta tattara, Hukumomi a kasar Ukraine sun tabbatar da cewa sojojin Rasha sun kutsa arewacin Birnin Kyiv.

A halin yanzun Motocin yaƙin sojojin Rasha sun shiga cikin babban birnin ta hanyar arewacin Kyiv, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Shugaban ƙasar Ukraine Zelensky ya yi jawabi ga mutanen kasar tun ɗazun kuma ya yi kira ga shugaban Rasha Putin ya dakatar da wannan yaƙin ya duba yuwuwar tsagaita wuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel