Gwamnatin Buhari Ta Faɗa Wa Rasha Ta Janye Sojojinta Daga Ukraine

Gwamnatin Buhari Ta Faɗa Wa Rasha Ta Janye Sojojinta Daga Ukraine

  • Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta saka baki cikin rikicin da ke faruwa tsakanin kasar Rasha da Ukraine tana mai kira ga Rasha ta mayar da dakarunta gida
  • Najeriya ta yi wannan kiran ne a wani taro da ta yi da wakilan kasashen G7 a ranar Juma'a a Abuja inda ta yi kira da bangarorin biyu su rungumi diflomasiyya da zaman lafiya
  • Jakadan Jamus kuma shugaban G7, Birgitt Ory, ya yi wa Najeriya godiya bisa tofa saka baki a lamarin tana mai cewa muryar Najeriya na da muhimmanci a duniya kuma ya dace a ji matsayarta

Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta gana da wakilan kasashen G7 a Najeriya inda ta nuna damuwar ta game da rikicin Rasha da Ukraine tana mai kira da a warware lamarin cikin zaman lafiya, rahoto Daily Trust.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya ajiye siyasa, ya ba Buhari shawara a kan rikicin Rasha v Ukraine

Ministan harkokin kasashen waje, Goeffrey Onyeama, ya gana da wakilan a ranar Juma'a a Abuja, yana mai cewa gwamatin Najeriya ta yi kira da a zauna lafiya kuma a yi amfani da diflomasiyya da wurin warware matsalar cikin lumana.

Gwamnatin Buhari ta fada wa Rasha ta janye sojojinta daga Ukraine
Gwamnatin Najeriya ta fada wa Rasha ta janye sojojinta daga Ukraine. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Onyeama ya ce Najeriya bata goyon bayan matakin da Rasha ta dauka na amfani da karfin soji, tana mai kira ga Rasha ta janye dakarunta, rahoton The Punch.

"Dukkan bangarorin biyu su mayar da hankali wurin zaman lafiya da diflomasiyya.
"Muna goyon bayan duk wani mataki na dakatar da harin soji kuma dakarun Rasha su janye su koma Rasha," a cewar Onyeama.

Jakadan Jamus ya yaba da matsayar Najeriya kan rikicin na Rasha da Ukraine

Da ya ke magana da manema labarai bayan taron na sirri, Jakadan Jamus a Najeriya, Birgitt Ory, wanda kuma shine shugaban G7 ya yaba da matakin Kungiyar Hadin kan Afirka, AU, kan rikicin.

Kara karanta wannan

Duk wanda yayi mana shisshigi kan yakinmu da Ukraniya zai fuskanci ukuba, Shugaban kasan Rasha

Ory, wanda kuma ya jinjinawa Najeriya kan tofa albarkacin bakinta, ya ce Najeriya muhimmiyar murya ce da ya dace duniya ta ji daga gare ta.

Ya ce abin da ke a fili shine tir da hare-haren da dukkanin kasashen Majalisar Dinkin Duniya suka yi sakamakon harin da Rasha ta kai.

Ory ya ce matakan da Majalisar Dinkin Duniya da Kwamitin Kare Hakokin Bil Adama, wacce Najeriya mamba ce da wasunsu suka dauka yana da muhimmanci.

Sauran wadanda suka hallarci taron sun hada da jakadun Amurka, Birtaniya, EU, ECOWAS, Japan da Canada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel