Bidiyon kayataccen otal din da aka mayar da gidan Nelson Mandela ya janyo cece-kuce

Bidiyon kayataccen otal din da aka mayar da gidan Nelson Mandela ya janyo cece-kuce

  • Yanzu an mayar da gidan shugaban kasan Afirika ta kudu na farko, marigayi Nelson Mandela, zuwa Otel mai suna Santuary Mandela
  • Dalilin canza tsarin ginin shi ne, tsare wa gami da girmama martabar shugaban abin koyin wanda yayi yaki da banbancin launin fata
  • Masu amfani da kafafan sada zumuntar zamani sun yi tsokaci, yayin da suke ganin da alamu an yi hakan ne don jin dadin masu hannu da shuni kadai

Shugaban kasar Afirika ta kudu na farko, marigaya Nelson Mandela, ya kafa tarihin da zai dauki tsawon zamani ba a manta ba.

Don killace wa gami da martaba tarihin da shugaban kuma abun koyin ya kafa, an maida gidan shi, wanda shine alamar mulkin shi da kuma yaki da nuna bambamcin launin fata zuwa tsadajjen Otel a matsayin abunda zai wakilci yaki akan bambamcin launin fata.

Kara karanta wannan

Shiga tashin hankali: Abba Kyari da jiga-jigai 6 da suka fada rashin lafiya yayin bincikarsu

Bidiyon kayataccen otal din da aka mayar da gidan Nelson Mandela ya janyo cece-kuce
Bidiyon kayataccen otal din da aka mayar da gidan Nelson Mandela ya janyo cece-kuce. Hoto daga @ReutersAfrica
Asali: Twitter

Yayin da ake tunanin cigaban zai zama abun burgewa, masu amfani da kafafan sada zumuntar zamani ba su yaba da hakan ba, inda suke ganin tsarin da aka sake ba a yi don abunda gwarzon jarumin yayi fafutuka akai ba. Kuma masu arziki ne kadai zasu amfana. Ga wasu daga cikin tsokacin da sukayi akan wallafar:

@cvaaustin ya ce: "A ra'ayi na, cin zarafin sa ne da tsabar bayyanar da fifikon mai kudi a kan talaka. Zai fi dace wa a ce gidan tarihi aka yi, amma hakan ba zai kawo kudi ba."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

@LeftistWeebBLM ya mayar da martani da: "A tunani na, masu hannu da shuni ne kadai za su iya tantance tarihin da ya kafa, meyasa suke murnar nuna daidaito tsakanin 'yan kasa da bayyana bambamcin?
@NodinNganji ya yi tsokaci da: "Abun ban takaicin shi ne, kungiyar da ke kula da wannan "kasaitaccen Otel din" (Kungiyar kasuwancin Motsamayo) Kashi 46 cikin 100 ne na bakar fata.

Kara karanta wannan

Babban dalilin da yasa Gwamnatin Buhari ba zata yi sulhu da yan bindiga ba, Minista ya fasa kwai

Mandela yayi yaki ne a kan nuna bambamcin launin fata, amma ga kungiyar shi wacce kungiyar hadin guiwar branco ke jagoranta sun sa ribar da ke sama da tarihin da ya kafa, kuma sun haramta wa mutane damar sanin shi sosai."
@CosThislsAfrica ya rubuta: "Dama can akwai wani gidan tarihi a kungiyar Nelson Mandela, wacce ba ta wuce tazarar layika biyu daga can ba ( kada mu ambaci dayan gidan tarihin Mandela mai nisan tazarar minti 30 a abun hawa cikin Soweto). Sun yi kokari sosai na adana ginin daga tashi aiki gaba daya. Dama Tbf dake Joburg suna da gidajen tarihin Mandela da yawa."

Bidiyon Obasanjo ya na kwasar rawa, ya doke jarumar fim a iya fitar da salo

A wani labari na daban, Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban kasar Najeriya mai shekaru tamanin da hudu ya bayyana salonsa da irin karfi da jikinsa ke da shi tamkar matashi a wurin rawa da jaruma Adedoyin Kukoyi.

Kara karanta wannan

NDLEA ta cafke kudi har $4.7 na jabu a Abuja, ta yi ram da maijego dauke da kwayoyi

Bidiyon mai nishadantarwa da bada dariya ya nuna tsohon shugaban kasar da jarumar inda suke girgijewa.

Sun yi rawa ne ga wani kidan Yarabawa inda ganguna masu yawa da zaki ke buga musu sauti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel