Bidiyon Obasanjo ya na kwasar rawa, ya doke jarumar fim a iya fitar da salo

Bidiyon Obasanjo ya na kwasar rawa, ya doke jarumar fim a iya fitar da salo

  • Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana a matsayin wanda ya lashe gasar rawa tsakaninsa da jarumar Nollywood Adedoyin Kukoyi
  • A wani bidiyo mai nishadantarwa da bada dariya da ke ta yawo a kafar sada zumunta, an ga Obasanjo ya na juyi wurin rawa wanda ya sanya jama'a ihu
  • Amma ana dab da gangar za ta tsaya da kida a shagalin bikin, Obasanjo ya tsinkayi wurin rawan da irin salonsa mai bada mamaki

Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban kasar Najeriya mai shekaru tamanin da hudu ya bayyana salonsa da irin karfi da jikinsa ke da shi tamkar matashi a wurin rawa da jaruma Adedoyin Kukoyi.

Bidiyon mai nishadantarwa da bada dariya ya nuna tsohon shugaban kasar da jarumar inda suke girgijewa.

Sun yi rawa ne ga wani kidan Yarabawa inda ganguna masu yawa da zaki ke buga musu sauti.

Kara karanta wannan

Kaduna: Ina shirin aurar da 2 daga cikin 'ya'yana mata da aka sace, Basarake

Bidiyon Obasanjo ya na kwasar rawa, ya doke jarumar fim a iya fitar da salo
Bidiyon Obasanjo ya na kwasar rawa, ya doke jarumar fim a iya fitar da salo. Hoto daga @doyinkukoyi
Asali: Instagram

Obasanjo ya yi juyi tamkar karamin yaro

A yayin rawar da ta birge masu kallo kuma ta saka suka dinga ihu da tafi ga tsohon shugaban kasan, an ga Obasanjo ya yi juyin masa a filin rawar.

Obasanjo ya bayyana a filin rawan

Amma a yayin da kidan ya shige shi aka yi kuma wata irin kida, tsohon shugaban kasan ya tsaya sannan ya cigaba da girgijewa.

A yayin wallafa bidiyon, Adedoyin Kukoyi ta rubuta:

"Ni da kaina na bukaci mu yi rawa kuma babu wasa ya amsa kirana. Masu kallo, ga rawa na da tsohon shugaban kasar Najeriya, Chief Olusegun Okikiola Aremu Obasanjo."

Ga bidiyon a kasa:

Bidiyon biloniya Dangote ya na kwasar rawa a wurin wani biki ya kayatar

A wani labari na daban, nishadi ba ya kebantuwa ga talaka ko mai arziki, komai arzikin mutum, ya na bukatar nishadi a wasu lokutan. Idan aka yi maganar hamshakin mai arziki kamar Alhaji Aliko Dangote, wasu za su ce ba shi da lokacin halartar bukukuwa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Bayan Ahmed Musa, Wani Ya Sake Yi Wa Tsohon Dan Wasan Super Eagles Kyautar Naira Miliyan 1

Sai dai ba hakan ba ne ga hamshakin mai arzikin Afrikan kuma bakar fatan da ya fi kowa arziki a duniya, ya na shiga nishadi a lokuta da dama.

Bidiyon biloniya kuma hamshakin mai arzikin Afrika, Alhaji Aliko Dangote, ya na kwasar rawa cike da birgewa a wurin wani biki ya matukar kayatarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng