Satar Abacha: Najeriya ta dauki Lauya, za tayi shari’a da kasar Birtaniya a kan €180m

Satar Abacha: Najeriya ta dauki Lauya, za tayi shari’a da kasar Birtaniya a kan €180m

  • Najeriya ta na neman a fito da wasu kudin da ta ke zargin Sani Abacha ya boye a kasar Birtaniya
  • Gwamnatin Tarayya ta dauki hayar lauya da zai yi shari’a da hukumar NCA ta kasar Ingila a kotu
  • Tun a 2018 ake so wadannan kudi har €180m su dawo cikin asusun Najeriya, amma abin ya gagara

Gwamnatin Najeriya za ta shiga kotu da hukumar NCA mai binciken mai laifuffuka a Birtaniya a kan wasu kudi da ake zargin su Sani Abacha sun boye a Ingila.

Wani rahoto da ya fito daga jaridar The Telegraph ta kasar Ingila ya bayyana cewa za ayi shari’a tsakanin gwamnatin tarayya da NCA a kan wadannan kudin

Legit.ng ta fahimci wadannan kudi da ake rigima a kansu har miliyan €180 ko miliyan £150 sun kai kimanin Naira biliyan 85 a yadda kasuwar canji ta ke a yau.

Kara karanta wannan

Jonathan: Asalin abin da ya sa na kirkiro makarantun Almajirai a Arewa a mulkina

Akwai wani babban ‘dan siyasar kasar nan da ake zargin ya taimakawa Marigayi Janar Sani Abacha wajen fita da biliyoyi, aka boye su a bankunan ketare.

Najeriya da National Crime Agency

National Crime Agency ta Ingila ta samu labarin wadannan kudi, kuma ta garkame asusun da su ke ciki. Wadannan kudi ne Gwamnatin Najeriya take so su fito.

Shugaban Najeriya
Buhari a hanyar Turai Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Arise TV ya ce ana samun ja-in-ja tsakanin Najeriya da hukumar NCA ta Ingila domin ganin an dawo da wadannan biliyoyin, an damkawa gwamnatin tarayya.

Tun tuni shugaba Muhammadu Buhari yake ta kokarin ganin wadannan kudin sun fito. Amma hukumomin kasar Birtaniya da Amurka su na kawo masa cikas.

$311bn sun fito a 2020

A watan Mayun 2020 ne gwamnatin tarayya ta karbi wasu Dala miliyan $311 daga cikin kudin da ake tunanin tsohon shugaban kasa Sani Abacha ya boye a ketare.

Kara karanta wannan

Shugaban NNPC ya bayyana wadanda suka shigo da rubabben fetur daga kasar waje

A daidai wannan lokaci akwai kotun Ingila da ke sauraron karar wasu kudi miliyan €90 da ake zargi Sani Abacha ya wawura da sunan kudin tsaro a Najeriya.

Wannan karo Najeriya ta dauki hayan kwararran lauya, Kingsley Napley domin kare ta a kotu. Da The Telegraph ta tuntubi hukumar NCA, ba ta iya cewa komai ba.

Atiku Bagudu

Mai girma Gwamna Atiku Abubakar Bagudu ake zargin ya taka rawar gani wajen sace dalolin. Zargin da Sanata Bagudu na jihar Kebbi ya karyata tun ba yau ba.

Kamfanin The Bagudu brothers enlisted Farrer & Co sun dauke fam miliyan €98 daga British Virgin Islands zuwa wasu tsibiri a kasashen waje, sun birne su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel