Naziru sarkin waka ya yiwa Ladin Cima da Fati Slow kyautan miliyoyi naira

Naziru sarkin waka ya yiwa Ladin Cima da Fati Slow kyautan miliyoyi naira

  • Mawaki Naziru Sarkin waka tare da yayyensa da ke masana'antar Kannywood sun baiwa dattijuwar jaruma, Ladin Cima kyautar naira miliyan biyu domin ta ja jari
  • Hakazlika Naziru ya yiwa Fati Slow wacce ta caccake shi kan furucin da ya yi a baya kyautar naira miliyan daya domin itama ta ja jari
  • Mawakin ya kuma bayar da hakuri a kan furucin da ya yi a baya wanda ya haddasa cece-kuce

Mawakin Kannywood, Naziru Sarkin waka ya tare da yayyensa da ke masana'antar shirya fina-finan sun yi wa dattijuwar jaruma, Ladin Cima kyautar kudi naira miliyan biyu.

Naziru a cikin bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Instagram, ya ce sun yi mata kyautar wannan kudi ne domin ta ja jari ta yadda za ta dunga samun na cin abinci. Ya kuma ce idan Allah ya barsu da rai za su dunga tallafa mata lokaci zuwa lokaci.

Kara karanta wannan

Sabon salo: Bidiyon yadda aka raba danyen timatir da attarugu a wajen wani biki

Naziru sarkin waka ya yiwa Ladin Cima da Fati Slow kyautan miliyoyi naira
Naziru sarkin waka ya yiwa Ladin Cima da Fati Slow kyautan miliyoyi naira Hoto: BBC Hausa
Asali: UGC

Hazalika ya ce an tura masa bidiyon abokiyar sana'arsa Fati Usman wacce aka fi sani da Fati Slow inda take ta raddi kan furucin da yayi a baya game da yadda ake lalata da mata a masana'antar.

Ya ce shi maganar da Fatin tayi bai dame shi ba domin a ganinsa tana bukatar taimako ne. Don haka ya bata kyautar naira miliyan daya domin ta ja jari itama.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cikin bidiyon, an gano Naziru yana cewa:

“Ita wannan mata, da ni da yayyen nawa da ake ta ganin mun yi, mun yanke shawara idan dai harkar fim ce, abinci ne yake kawota ta nema ta ci, farko mun ware mata naira miliyan biyu ta je ta fara jari, kafin mu ga me Allah zai yi. Sannan nan wani taimako za mu dunga yi mata.

Kara karanta wannan

TY Shaban ya gasgata maganar Naziru, ya bukaci ya rantse bai taba neman wata jaruma da lalata ba

“Wannan idan dai abinci ne yake kawo ta masana’antar nan, neman abun da za ta sa a baki, Allah ya bamu tsawon rai, Ya kuma ci gaba da dafa mana za mu kula da lamarin.
“Sannan kamar dazu ana ta turo mun da bidiyon Fati Slow. Fati ta dan jima a masana’antar don lokacin tun kan nayi suna tana ciki. Duk wannan abun da Fati take yi ba wani abu bane, idan mutane sun kalle shi ya yi kama da abubuwan da za a ce tana bukatar taimako. Toh itama wannan maganar tata ta jawo mata a zo ayi kwamitin da za su karba mata naira miliyan daya a san sana’ar da za ta yi.
“Ni nayi alkawarin zan bata miliyan, maganar da tayi kuma, itama Allah zai kula da lamarin. Allah ya bamu dacewa."

Kuyi hakuri, amma gaskiya na fadi: Sarkin Waka ya saki sabon bidiyo, ya yi sabon bayani

Kara karanta wannan

Babu dan fim da ya tumbatsa duniya ta san shi da zai ce iya kudin fim ke rike shi – Rukayya Dawayya

A baya mun ji cewa shahararren mawakin Hausa kuma jarumi a kannywood, Naziru Ahmad wanda aka fi sani da sarkin waka, ya ba jama’a hakuri a kan kalaman da ya yi halin masana’antar ke ciki.

Naziru ya bayyana cewa shi bai yi furucin don lalata sana’ar kowa ba illa kawai ya ce iya gaskiyarsa ya fada.

Jarumin a cikin sabon bidiyon da ya saki, ya ce shi bai yi don wani ya so shi ko don wani ya ki shi ba, cewa akwai bukatar ayi gyara ne shiyasa ya fada ma al’umman gari halin da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel