Amarya ta hana babbar kawarta halartar shagalin bikinta saboda ta caba adon da yafi nata

Amarya ta hana babbar kawarta halartar shagalin bikinta saboda ta caba adon da yafi nata

  • Wata amarya ta janye gayyatar da ta yiwa kawarta zuwa wajen shagalin bikinta
  • Hakan ya kasance ne bayan ta yi zargin cewa kawar tata ta caba adon da ya fi nata
  • Sai dai hakan bai yi wa kawar dadi ba inda a yanzu suka raba jiha domin tana ganin babu amfanin kawancen nasu

Jamus - An janye gayyatar da aka yiwa wata kawar amarya zuwa wajen biki saboda ta fi amaryar haduwa.

Wata yar kasar Jamus mai suna Alena Yildiz, ta bayar da labarinta cewa:

“Kawata ta kut da kut ta janye gayyatar da tayi mun zuwa wajen bikinta saboda tana ganin nayi kyau da yawa a kayan da ya zabar mun.”
Amarya ta hana babbar kawarta halartar shagalin bikinta saboda caba adon da yafi nata
Amarya ta hana babbar kawarta halartar shagalin bikinta saboda caba adon da yafi nata Hoto: Lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Ta kara da cewa:

Kara karanta wannan

Daga karshe kungiyar IPOB ta bayyana masu daukar nauyinta

“Duk da haka na dauki wasu zafafan hotuna a cikinsa.”

Yildiz ta bayyana cewa sauran kawayen amaryar ma sun sanya hadaddun kaya amma amaryar bata ga aibunsu ba sai nata sannan ta mayar da ita saniyar ware, shafin lindaikejisblog ta rahoto.

Kawar amaryar ta ce:

“Duk sauran kawayen amaryar sun sanya hadaddun kaya suma, amma nawa ne kawai ya tsone mata ido.”

Yildiz ta yi ikirarin cewa amaryar bata yarda da kanta ba sannan ta fada mata cewa kayan zai ja hankali da yawa.

Kawar amaryar ta ga laifinta inda tace da ta san cewa kayan zai yi wa wata daga cikinsu kyau da yawa, da ta zabi kaya mara fasali.

A halin da ake ciki, kawance ya kare tsakanin Yildiz da amaryar, rahoton topnaija.ng.

Yildiz ta ce:

“Hakan ya sa na ji kamar bani da wani amfani da nake da shi a matsayin kawarta.”

Ba ma son 'yar mu ta sha wahala: Iyayen amarya sun fasa aurawa ango 'yarsu bayan ganin gidan da za ta zauna

Kara karanta wannan

Matasa sun shiga hannu yayin da suke kokarin satan kaya a wurin gobara a Abuja

A gefe guda, wata budurwa ‘yar Najeriya mai suna Maryam Shetty a Facebook ta yada wani labari a shafinta, inda ta zayyana yadda aka fasa wani aure bayan samun karamar matsala.

Kafin ta ba da labarin, budurwar ta rubuta cewa al'adar nuna fifiko ya zama ruwan dare a yankin Arewacin kasar nan kuma iyaye ne ke aiwatar da shi.

Ta bayyana cewa kafin a soke auren, iyayen amaryar sun ji cewa gidan angon sam bai musu ba, kuma bai dace da matsayin ’yar su ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel