Babbar harka: Yadda kamfanin Facebook ke saye duk wani abu mai suna 'Meta' a duniya

Babbar harka: Yadda kamfanin Facebook ke saye duk wani abu mai suna 'Meta' a duniya

  • Meta, mamallakin Facebook, Instagram, Messenger da WhatsApp yana kan hanyar siyan duk wani abu mai suna Meta
  • Kamfanin ya buya a bayan wani kamfani don neman sayen wani banki mai suna Meta a kan kudi Naira biliyan 29.9 kawai don Mark ya mallaki suna Meta
  • Kamfanin Mark Zuckerberg yana son aiwatar da nufinsa na metaverse, inda mutane za su iya amfani da fasahohin AI da AR don yin abubuwa iri-iri daban-daban

Meta, a baya wato Facebook, na cikin gaggawa don siyan hajoji a ko'ina cikin duniya matukar sunansu Meta.

Kamfanin wanda ya mallaki wasu kafafen sada zumunta na zamani yana kan kokarin saye wani banki mai suna Meta Financials, kamar yadda kakakin bankin ya fada wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Litinin, 13 ga Disamba, 2021.

Mamallakin kamfanin Meta, Mark Zuckerberg
Babbar harka: Yadda kamfanin Facebook ke saye duk wani abu mai suna 'Meta' a duniya | Hoto: Mark Zuckerberg
Asali: UGC

Meye ke cikin suna?

Yarjejeniyar cinikin ta nuna mahimmancin sunan Meta, da kuma irin yadda Mark Zuckerberg wanda ke kan yunkurin aiwatar da metaverse ke son sunan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meta Financials ta bayyana haka ne a wata takarda da ta fitar a ranar Litinin, 13 ga Disamba, 2021, cewa wani kamfani a Delaware mai suna Beige Key LLC ya amince ya sayi sunan bankin a kan tsabar kudi Naira biliyan 29,9.

Masu sharhi na zargin cewa Beige Key na iya kasancewa na da alaka da katafaren dandalin sada zumunta mallakar Mark Zuckerberg.

Abin da Facebook ke cewa

"Beige Key yana da alaka da mu kuma mun sayi wadannan kadarorin alamar kasuwanci."

Meta Financials, ta hanyar reshensa, yana gudanar da ayyukan banki kamar ajiya, lamuni da katunan kudi da lamunin kasuwanci.

Meta Financials ya hada kai da abokan hulda ciki har da hukumomin gwamnati da kamfanonin fasahar kudade don gudanar da ayyukan banki tare da manufar habaka hadakar kudi.

A cewar wata sanarwa da Faceboom ta fitar a watan Oktoba, kamfanin ya canza suna zuwa Meta Platforms sannan ya zuba hannayen jari masu yawa a fannin intanet ta wayar hannu.

Meta, wanda ya karu wajen samun kudin shiga fiye da kamfanoni a Silicon Valley da yawa kuma wanda za ke bukatar hadin gwiwa tsakanin kwararrun masana fasaha, na iya wuce shekaru goma don samun cikakkiyar fahimta.

Mai Facebook ya magantu

Kakakin kamfanin Meta Platforms ya ce kamfanin ya shiga tattaunawa da Meta Financial kafin a sanar da canza sunan Facebook.

A cike-ciken takardu, bankin ya ce ya fara duba ga dabarun sauya suna a farkon wannan shekarar, amma mai magana da yawun MetaBank ya ki cewa komai game da tattaunawar baya ga abubuwan da ke cikin cike-ciken.

Hannun jarin bankin yana gudana a kasuwa akan 1.5% cikin 100% da tsakar yammacin ranar Litinin, 13 ga Disamba, 2021, wanda ya ba shi darajar kasuwa kusan dala biliyan 1.74. Meta Platforms ya karu da 1.6%, wanda aka kimanta akan dala biliyan 933.

Wanda yace shi ya kirkiro Bitcoin ya gagara cire kudi a asusu a kasuwar Crypto

A wani labarin, Craig Wright, wanda ya ayyana kansa a matsayin wanda ya kirkiri Bitcoin, yana shirin kaura zuwa wani kauye bayan ya ci nasara a kotu inda ya ce an ayyana shi a matsayin wanda ya kirkiro bitcoin.

Duk da yanke hukuncin, al'ummar Bitcoin ba su gamsu ba kuma sun kalubalance shi da ya aika wani kaso na Bitcoin miliyan 1.1 da ya ce yana da ikon akai zuwa wani asusu don nuna ikon mallakarsa.

Indiatimes ta ce al'ummar Bitcoin ba su amince da Wright ba, kuma mutane da yawa sun nemi kawai ya motsa wani dan karamin kaso na Bitcoin kamar miliyan 1.1 zuwa wani asusu na daban don tabbatar da mallakar tsabar, lamarin da ya faskara ya zuwa yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel