An haramta wa kwastoma shiga wurin cin abincin 'ci iyakar iyawar ka' saboda mugun ci

An haramta wa kwastoma shiga wurin cin abincin 'ci iyakar iyawar ka' saboda mugun ci

  • Wani mutum mai suna Kang an haramta masa shiga wani gidan cin abincin 'ci iyakar iyawarka' a kasar China saboda mugun ci
  • An gano cewa, Kang ya lamushe 1.5Kg na naman alade a ziyararsa ta farko yayin da ya lashe 4Kg na kaguwa a ziyararsa ta biyu
  • Kang wanda ya kasance masoyin abinci, ya yi martani kan hana shi shiga wurin inda yace an nuna masa wariya ne karara

China - Mugun cin wani mutum ya janyo aka haramta masa shiga wani gidan cin abinci a kasar China har abada.

Mashable sun ruwaito cewa, Kang maciyin abinci ne na gaske kuma gidan cin abinci na duk abinda za ka iya ci mai suna Handadi Seafood BBQ Buffet sun hana shi shiga.

Kara karanta wannan

Yadda dan Najeriya ya zama sanata a Turai, ya kware a girki, kuma yake so ya gaji Buhari

Maigidan abinci ya haramta wa kwastoma zuwa cin abincin har abada saboda mugun ci
Maigidan abinci ya haramta wa kwastoma zuwa cin abincin har abada saboda mugun ci. Hoto daga sea.mashable.com
Asali: UGC

Mugun cin abincinsa ne ya janyo hankalin mai gidan cin abincin

Wani rahoto da BBC ta gano, ya nuna cewa Kang ya lamushe 1.5Kg na naman alade a ziyarar farko da ya kai wurin cin abincin kuma ya ci 4Kg na kaguwa a ziyara ta biyu da ya kai.

Wannan mugun cin ne ya janyo hankalin mai gidan cin abincin inda ya yi hanzarin daukar matakin nan mai bada mamaki.

A yayin jawabi kan mugun cin Kang, mai gidan cin abincin ya ce a gaskiya kudinsa na karewa idan aka alakanta da sauran masu zuwa.

Wannan mugun cin ne ya janyo hankalin mai gidan cin abincin inda ya yi hanzarin daukar matakin nan mai bada mamaki.

Mai gidan cin abincin ya zargi Kang da barnatar da abincin, zargin da ya musanta a take.

Kara karanta wannan

Ka ba coci kason ta daga kudin da abokai suka hada maka, ko ka shiga wuta, Fasto ga Davido

Wannan abu bai yi wa Kang dadi ba

A martaninsa yayin zantawa da manema labarai, Kang ya caccaki gidan cin abincin inda ya zargesu da nuna banbanci.

Ya kara da cewa, wannan al'amarin bai taba faruwa da shi ba a yayin da ya ke ziyartar wasu wuraren cin abincin.

"A gaskiya ina ganin wannan gidan cin abincin ba zai iya yin abinda yayi alkawari ba," yace cike da fushi.

Mene ne gidan cin abincin 'ci iyakar iyawar ka'

Fitattun gidajen cin abinci a yankin nahiyar Asia masu tambarin "ci iyakar iyawar ka" an yi su ne inda kwastoma zai biya kudi amma ya ci duk abinda ya ke so kuma iyakar yadda zai iya.

Saurayi ya tsere bayan budurwa ta debo 'yan uwanta 23 sun kwashi gara suna jiran ya biya

A wani labari na daban, wata budurwa ta gayyaci 'yan uwan ta 23 a haduwar farko da za su yi da sabon saurayin ta domin gwada karamcinsa amma sai reshe ya juye da mujiya.

Kara karanta wannan

Ra'ayi: Bidiyon matashin da ya bar sana'a ya koma zaman don kallon jiragen kasa

Budurwar za ta fara haduwa ne da matashi mai suna Lui mai shekaru 29 a wani wurin cin abinci da ke gabashin yankin Zhejiang na kasar China kamar yadda mujalllar yankin, Taizhou ta wallafa, LIB ta wallafa.

Mahaifiyar Lui ce ta hada shi da budurwar ganin cewa dan ta ya na ta girma kuma babu budurwa balle batun aure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel