Saurayi ya tsere bayan budurwa ta debo 'yan uwanta 23 sun kwashi gara suna jiran ya biya

Saurayi ya tsere bayan budurwa ta debo 'yan uwanta 23 sun kwashi gara suna jiran ya biya

  • Wata budurwa ta kwashi 'yan uwan ta 23 domin haduwar farko da saurayi a wurin cin abinci, ta ce gwada karamcinsa ta ke
  • Saurayi Lui kuwa ya cika wandonsa da iska bayan ganin zugar 'yan uwanta da ta kwaso kuma suka ci abincin $3,100, kusan N2m
  • Matashi Lui mai shekaru 29 ya ce babu shakka ya yi niyyar biyan kudin duk abinda za su ci, amma bai yi tsammanin 'yan uwan ta za ta kwaso ba

China - Wata budurwa ta gayyaci 'yan uwan ta 23 a haduwar farko da za su yi da sabon saurayin ta domin gwada karamcinsa amma sai reshe ya juye da mujiya.

Budurwar za ta fara haduwa ne da matashi mai suna Lui mai shekaru 29 a wani wurin cin abinci da ke gabashin yankin Zhejiang na kasar China kamar yadda mujalllar yankin, Taizhou ta wallafa, LIB ta wallafa.

Kara karanta wannan

Bidiyon budurwar da ta yarfa saurayinta cikin mutane yayin da ya yi mata tayin aure, ta ƙwace zoben ta jefar a ƙasa

Saurayi ya tsere bayan budurwa ta debo 'yan uwanta 23 sun kwashi gara suna jiran ya biya
Saurayi ya tsere bayan budurwa ta debo 'yan uwanta 23 sun kwashi gara suna jiran ya biya. Hoto daga recetasnestle.com.co
Asali: UGC

Mahaifiyar Lui ce ta hada shi da budurwar ganin cewa dan ta ya na ta girma kuma babu budurwa balle batun aure.

A kokarin shi na birge sabuwar budurwsar shi, ya amince zai biya kudin duk abincin da za su ci, ashe bai san za ta kwaso zugar 'yan gidansu ba ne.

Sai dai kuma, ganin yawan mutanen da budurwar ta kwaso, matashin ya tsere tare da barin budurwar ta biya kudi har $3,100 wanda 'yan uwan ta suka ci abincin shi.

Matar ta yi wa kafafen yada labaran yankin bayanin cewa ta so gwada karamcin sabon saurayin na ta ne kafin ta amince su cigaba da soyayya.

An wallafa labarin budurwar a Weibo kuma ya yadu tare da samun sama da mutum miliyan dari biyu da sittin da suka duba tare da tsokaci.

Kara karanta wannan

Jigo a kudu ya gano hanyar lallabar 'yan Arewa su mika mulki kudu a 2023

Wasu daga cikin masu tsokacin sun dinga sukar budurwar, yayin da wasu suka dinga yaba wa Lui.

"Ko wawa ba zai taba kwaso mutum 23 ba domin haduwa da saurayi," wani mai tsokaci yace.

Saurayi ya biya kudin abincinsa shi kadai bayan budurwa ta je mishi da kawaye 2

A wani labari na daban, cikin takaici da alhini wata budurwa mai amfani da suna Reddishwine3 a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter ta bayyana yadda saurayinta ya tozartata a gaban kawayenta.

Ta ce sun yi za su fita cin abinci ita da saurayinta, sai ta gayyaci kawayenta suka tafi tare. Sai da suka kammala cin abincin tas, ya mike tsaf ya tafi ya biya kudin nashi abincin ya bar su a nan.

Ta yi wallafar ne ranar Juma'a, 8 ga watan Janairu, inda tace lallai wasu mazan ba su da tausayi balle imani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel