Matar da ta siya wa mijinta mota ta ce za ta iya siya masa jirgin sama idan tana da hali

Matar da ta siya wa mijinta mota ta ce za ta iya siya masa jirgin sama idan tana da hali

  • Wata 'yar Najeriya da ta saya wa mijinta sabuwar mota kirar Mercedes Benz ta ce za ta iya saya masa jirgin sama idan Allah ya albarkace ta
  • Matar mai suna Gbadewole Olubunmi Mary ta ce mijinta mai kyauta ne amma mutane ba sa ba shi kyaututtuka
  • A cewar Mary, ta kasance tana ta shirye-shiryen farantawa mijinta rai da babban kyauta tun haihuwar ɗansu na fari

Wata ‘yar Najeriya Gbadewole Olubunmi Mary da ta bai wa mijinta kyautar sabuwar mota kirar Mercedes Benz a ranar zagayowar ranar aurensu na 7, ta ce za ta so yi masa kyautar jirgin sama idan Allah ya albarkace ta.

Da take magana da @bbcnewsyoruba, matar ta ce ta saya wa mijinta motar ne saboda shi mutum ne mai kyauta.

Read also

Yadda 'Ruwa mai tsarki' ya raba Mata da Miji da suka shekara 10 suna gina soyayya

Matar da ta siya wa mijinta mota ta ce za ta iya siya masa jirgin sama idan tana da hali
Matar da ta siya wa mijinta mota ta ce za ta iya siya masa jirgin sama idan tana da hali Hoto: @bbcnewsyoruba
Source: Instagram

A cewar Mary, mutane ba sa ba mijinta kyaututtuka duk da cewa shi mutum ne mai bayarwa. Ta ce tana ta tunanin baiwa mutumin wani babban kyauta tun lokacin da suka haifi dan su na farko.

A kalamanta:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Tun lokacin da na sayi motar, na fahimci cewa soyayyar da yake yi min ya ƙaru. Tun daga lokacin yana ƙara nuna mun kulawa ta musamman. Ya kamata mutane su sani cewa idan suka ba mazajensu kyauta, daidai yake da ba wa kansu kyauta saboda miji da mata abu daya ne."

Mary ta shawarci mata da su kasance masu neman na kansu don siyawa kansu mutunci a cikin gidajensu.

Shi ma da yake magana, mijin Mary ya ce ya yi mamakin yadda matarsa ​​ta yi amfani da kuɗinta wajen samo masa mota. A cewarsa, ya dade yana jin dadin motar.

Read also

Magidanci ya kashe matarsa saboda ta raina bajintarsa wurin kwanciyar aure

Ya kuma ce motar na ahlin ne gaba daya, ya kara da cewa shi da matarsa ​​abokan aiki ne a ofishi daya.

@4lawiyo ya ce:

"Wannan abin burgewa ne ƙwarai, Allah Madaukakin Sarki ya ci gaba da ƙarfafa ƙaunar da kuke yiwa junanku."

@angelnikky75 yayi sharhi:

"Ina taya ki murna Allah ya kara maki albarka."

@nikkyshineshine ta rubuta:

"Ya yi kyau, hakan yana da kyau na yarda yana da kyau mata su tallafawa mazajen su, amma kamar yadd matar ta ce mijinta mai bayarwa ne kuma mutumin kirki ne."

@charlesbankole ya ce:

"Wannan yayi kyau. Na sani, matata za ta iya yin hakan itama. Jinjina ga irin waɗannan matan."

@realbabajide ya rubuta:

"Matar da ta cancanci ayi koyi da ita. Masu bayarwa ba sa rasawa. Sauya al’adar nan ta miji ke yin komai. Na san wasu za su dunga yi mata wani irin Kallo."

Bidiyon uwargida da ta fashe da kuka yayin da mijinta ya yi mata kyautar Venza tukwicin haifa masa ‘da

Read also

Ba zan iya zama da ita ba saboda bata yin wanka kullum, Miji ya nemi a raba aurensa da masoyiyar matarsa

A gefe guda, wani bidiyo mai kayatarwa ya burge jama’a inda wata 'yar Najeriya ta fashe da hawayen farin ciki bayan mijinta ya yi mata kyautar mota kirar Vanza a matsayin tukwicin haifa masa ‘da namiji.

A bidiyon da @sikiru_akinola ya yada a shafin Instagram, an gano matar da mijinta suna rawa yayin da yayi mata jagora zuwa wajen motar.

A cewar @sikiru_akinola, kyautar ta zo kwanaki hudu bayan matar ta haifi ‘da namiji.

Source: Legit

Online view pixel