Magidanci Ya Lakaɗa Wa Likitan Fata Mugun Duka Saboda Yaba Kyawun Fatar Matarsa
- ‘Yan sanda sun kama wani magidanci bayan ya daki wani likitan fata kamar bakon kare a asibitin da yake aiki
- Hakan ya biyo bayan yadda likitan ya yaba kyawun fatar matar sa wacce ta je asibitin don a duba lafiyar ta
- An samu bayanai akan yadda likitan ya yaba fatar ta bayan ya nemi ta nuna masa cikin ta, hannun ta da bayan ta
Kasar Rasha - ‘Yan sanda sun kama wani mutum bayan ya lakada wa likita dukan tsiya inda ya bar shi a mawuyacin hali bayan yabon kyawun fatar matar sa.
Matar wacce musulma ce mai sanye da hijabi ta sanar da mijinta, Bakhriddin Azimov cewa likitan fatar dan asalin kasar Rasha, Vladimir Zhirnokleev ya yaba kyawun fatarta.
Daga nan ne mutumin ya kai wa likitan farmaki, yanzu haka yana fuskantar hukunci akan cin zarafi kamar yadda LIB ta ruwaito.
Kamar yadda RT ta bayyana, lamarin ya auku ne a ranar Talata, 21 ga watan Satumba a Nizhnevartovsk dake Siberia.
Likitan ya ce ta duba lafiyar fatar ta ne kawai
A cewar Dr Zhirnokleev, ya umarci matar ta nuna masa hannun ta, cikin ta da bayan ta amma bai umarci ta nuna masa tsiraicin ta ba.
Bayan kammala duba jikin ta, ya shaida mata cewa babu wata matsala a fatar ta inda ya ce:
“Fatar ki tana da kyau.”
Saidai kamar yadda LIB ta ruwaito, matar ta kai wa mijin ta korafi inda ta ce likitan ya keta dokar musulunci.
Kamar yadda Azimov mai shekaru 29 ya bayyana:
“Ina da tabbacin likitan ya yaba da surar mata ta yayin duba lafiyar ta, hakan bai dace da tsari na ba.”
“Idan kai likita ne, ka yi aikin ka. Kada ka zake wurin tambayoyi da yaba surar jama’a don wannan ba aikin likita bane.”
Saidai Zhirnokleev ya tabbatar da cewa ya sanar da matar gaskiyar halin da fatar ta take ciki ne.
Kamar yadda jaridar Komsomolskaya Pravda ta ruwaito ya ce:
“Musulmai su dinga bi a hankali kuma cikin tsari wurin gyara akan lamurran da basu gane ba.
“Shiga ofishin likita da kuma naushin hancin sa bai dace ba bisa dabi’a da shari’a.
“Ni babba ne, ina da ilimi a fanni daban-daban, na kuma san abubuwa da dama na rayuwa kuma muna rayuwa ne a wurin da aka shimfida dokoki. Ya kamata jama’a su dinga bin dokoki.”
Yanzu haka an duba Zhirnokleev, yana fama da raunuka a kansa.
Asali: Legit.ng