Sani Hamza
5185 articles published since 01 Nuw 2023
5185 articles published since 01 Nuw 2023
Bill Gates ya bayyana rabuwarsa da Melinda a matsayin kuskuren da ya fi nadamar yi a rayuwarsa. Duk da haka, ya ce suna haɗuwa don kulawa da 'ya'yansu da jikoki.
Peter Obi ya ce shi bai kwallafa rai a kan lallai sai ya zama shugaban kasa ba amma yana bukatar Najeriya ta gyaru ta hanyar samar da shugabanci mai inganci.
CIA ta ce akwai yiwuwar COVID-19 ta samo asali daga dakin gwaje-gwaje a China, amma ba ta da tabbaci sosai, yayin da China ta musanta zarge-zargen nan gaba ɗaya.
Rikici ya kara tsananta a PDP yayin da 'yan kwamitin ayyuka na jam'iyyar suka ki amincewa da nadin lauyan da zai kare jam'iyyar a kotun koli, wanda Damagum ya zaba.
Gwamnan Dauda Lawal, ya bai wa dalibai 16 da suka yi karatun jinya daga Sudan aiki kai tsaye, yayin da ya jaddada cewa Zamfara ta ayyana dokar ta baci kan ilimi.
Fitaccen mawaki Senwele, daga jihar Kwara, ya rasu bayan 'yar gajeriyar rashin lafiya. An ce marigayin ya yi fice a salon wakokinsa na Dadakuada mai ban dariya.
Omowunmi Dada ta sha dakyar yayin da ta kamu da cutar sepsis yayin daukar fim a Oyo. An gano cewa cutar tana da matukar hatsari ga rayuwar mutum.
Asusun UNICEF ya ce yara 9.6% a Kano ne ke da iya karatu, yayin da ta ke ci gaba da inganta makarantu, horar da malamai, da samar da fasahar karatu ga yara.
Shugaba Tinubu zai halarci Taron Makamashi a Tanzania, inda zai yi jawabi kan kokarin Najeriya na samar da wuta ga kowa da inganta makamashi mai tsafta a Afirka.
Sani Hamza
Samu kari