Muhammad Malumfashi
17185 articles published since 15 Yun 2016
17185 articles published since 15 Yun 2016
A 2023, ba za ayi yunwa ba domin akwai isasshen kayan abincin da mutane za su ci. Ministan gona yace babu mamaki abinci ya kara tsada, amma da wahala a rasa.
Sadiq Ango Abdullahi ya fada hannun 'yan bindiga a watan Maris yayin da aka shirya zaben tsaida gwani na neman takarar majalisa a Mayu, sai ga shi ya samu tuta.
Ana tsoron cewa jami'an tsaro sun je gida sun dauke Yusuf Imam, wanda daya ne daga cikin masu taimakawa NNPP da dukiyarsu. Ogan boye ya nemi Sanata a NNPP.
Sai a jiya ne Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya ba Atiku Abubakar hakurin harin da aka kai masa a kamfe, amma ya fadawa ‘Yan adawa su cire rai da Borno.
Baffan Aminu Adamu wanda ake zargi da cin mutuncin Aisha Buhari a Twitter ya yi bayanin abin da ya auku, an ji da hannun Uwargidar shugaban kasa aka kama shi.
An shafe sama da shekaru 10 rabon da a karawa Likitoci albashi a Najeriya, a dalilin haka, likitoci 4000 sun shirya tafiya asibitocin ketare saboda su nemi kudi
Kasashen ECOWAS sun yi taro na musamman a babban birnin tarayya Abuja, Shugaba Muhammadu Buhari ne ya bude taron da jawabi, inda ya yi bayanin babban burinsa.
Ana zargin Jami'an tsaron SSS sun tasa keyar Aminu har fadar shugaban kasa, gaban Aisha Buhari inda suka rika jibgarsa, 'yan sanda sun ce sam babu ruwansu.
A watan Disamba, Bola Tinubu mai neman zama shugaban kasa a jam’iyyar APC zai dakatar da kamfe, zai tafi Amurka da Nahiyar Turai. Za a ji abin da zai kai shi.
Muhammad Malumfashi
Samu kari