Muhammad Malumfashi
20373 articles published since 15 Yun 2016
20373 articles published since 15 Yun 2016
Hukumar zabe ta INEC za ta fara rajistar masu zabe a dukkan jihohin Najeriya 36 da Abuja. Farfesa Mahmood Yakubu ya ce za a fara rajistar ne a ranar 18 ga Agusta.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka kwamandojin 'yan ta'adda a sassa daban-daban na kasar nan. Sojojin sun kuma cafke 'yan ta'adda masu yawa.
Bayan shirin Aliko Dangote na fara rarraba mai kai tsaye, Ƙungiyar dillalan mai ta NOGASA ta ce hakan zai iya haddasa karancin man fetur a ƙasar.
Tsohon sanatan Kogi ta Yamma, Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa haɗakar ƴan adawa za ta zaɓo wanda zai iya kifar da shugaban ƙasa Bola Tinubu a akwatun zaɓe.
Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya karyata rahotannin da ke yawo cewa ya gama shirin shiga jam'iyyar haɗaka ADC, ya ce yana nan daram a PDP.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya laftawa kasashe da dama haraji ciki har da Najeriya. Donald Trump ya kakaba harajin ne bayan wa'adin da ya bayar ya cika.
Kungiyar Muslim Public Affairs Centre (MPAC) ta ce harin dodon gargajiya kan limami ya saba wa doka ne kuma gwamnati ta binciki Lobanika da dukan masu hannu.
Tsohon Gwamnan Delta, James Ibori, ya koka kan matsin tattalin arziki da ake ciki a yanzu yayin ba da gudunmawar N100m a jami’ar Igbinedion domin tallafa mata.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sauya Nasir Gawuna, ya naɗa Air Vice Marshal Saddiq Ismaila Kaita (mai ritaya) a matsayin shugaban Majalisar Gudanarwa ta BUK.
Muhammad Malumfashi
Samu kari